Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Sanata Oluremi Tinubu Ta Tallafa Wa Ɗaliban FUDMA Da Miliyan 1

Daga Imrana Abdullahi Uwar gidan shugaban ƙasa, Sanata Oluremi Tinubu, ta bayar da tallafin karatu na Naira Miliyan Ɗaya ga ɗaliban Jami...

Daga Imrana Abdullahi

Uwar gidan shugaban ƙasa, Sanata Oluremi Tinubu, ta bayar da tallafin karatu na Naira Miliyan Ɗaya ga ɗaliban Jami'ar Gwamnatin tarayya ta Dutsinma, da ke Jihar Katsina kowannen su, waɗanda 'yan bindiga masu satar mutane suka sace kwanan baya, a ranar 4 ga watan Okutoba.

Uwargidan shugaban ƙasar, wacce ke tare da Mai ɗakin mataimakin shugaban ƙasa, Nana Shettima, a ranar Asabar a Abuja, sun miƙa wa kowane ɗaya daga cikin ɗaliban da aka kama Naira miliyan ɗaya da kuma na'ura mai ƙwaƙwalwa ( Kwamfuta), waɗanda aka sace lokacin suna a gidan da suke zaune a ranar 4 ga watan Okutoba.

Uwargida Oluremi ta kuma bayyana cewa, wannan tallafin gurbin karatu na kuɗi zai kasance ne na tsawon ahekaru huɗu, wanda kuma su ne shekarun da waɗannan yara za su kwashe a makarantar. Wato, Safiya Mutu, Hasiya Abubakar, Ramat Adam, Fatima Abdullahi da Fatima Mohammed

Dukkan waɗannan ɗalibai sun kasance suna matakin karatu aji na ɗaya ne, wato (100- level). Ta ce Gwamnatin tarayya na ganin muhimmancin karatun da suke yi da kuma tsaron lafiyarsu, saboda haka ne ta yi alƙawarin bayar da Naira Miliyan 2 ga Jami'ar. 

"Tun lokacin da aka ɗauke ku a ranar 4 ga watan Okutoba, muna cikin yanayi mai tsanani kuma na jin zafi sosai, tun daga kan iyayen ku, Malamanku da dai sauran yan Najeriya. 

"Kuma tun a wancan lokacin muka miƙa komai ga Allah da kuma jami'an tsaron mu muke ta yi masu addu'ar samun nasara, Allah ya sa ku dawo lafiya.

"Bayan samun aƙalla kwanaki 70 a hannun masu satar mutane suna yin Garkuwa da ku, sai ga shi a yau muna samun wata damar yin farin ciki da annashuwar dawowarku cikin al'ummar ƙasa".

"Za kuma mu ci gaba da duba ku sosai tun daga makaranta har zuwa samun ci gaban lafiyarku. 

"Samun ilimi mai inganci ne ainihin Makamin yaƙi da ta'addanci, don haka yana da matuƙar muhimmanci ku ci gaba da neman ilimi, ku tuna yadda rayuwarku take a can baya da kuma na al'ummar da kuke ciki da nufin yaƙi da ta'addanci da kuma sauran miyagun ɗabi'u baki ɗaya. 

"Muna fatan wannan jarabawar da kuka samu za ta ƙara maku ƙwarin gwiwar tashi tsaye wajen ayyukan ku da kuma karatun ku, ta yadda ƙasa za ta yi alfahari da ku."

Da yake gabatar da jawabi, wani babban jami'i a ofishin mai bayar da shawara a kan harkokin tsaro na shugaban ƙasa, Birgediya Janar Olutayo Adesuyi, cewa ya yi wannan taron haduwar da uwargidan shugaban ƙasa ta yi, abu ne mai matuƙar amfani, kasancewar lamarin ya nuna irin ƙoƙari da tausayin Gwamnatin tarayya, tare da taimaka wa waɗanda aka sace ɗin.

Da suke mayar da jawabi, kowace ɗaliba godiya ta yi ga uwargidan shugaban ƙasar bisa irin taimakon da ta yi masu.

No comments