Daga Ali Kakaki Magatakardar Hukumar Lura Da Aikin jinya da Unguwarzoma ta Nijeriya, Dr Faruq Umar Abubakar ya bayyana Shugaban Jami'ar ...
Daga Ali Kakaki
Magatakardar Hukumar Lura Da Aikin jinya da Unguwarzoma ta Nijeriya, Dr Faruq Umar Abubakar ya bayyana Shugaban Jami'ar Maryam Abacha da ke Kano, Farfesa Adamu Abubakar Gwarzo a matsayin mutum karimi, wanda ya san mutuncin jama'a.
Dr. Faruq ya yi wannan furucin ne a yayin da yake zantawa da manema labarai jim kaɗan da kammala bikin rantsar da ɗaliban da suka yi karatun jinya daga ƙasashe daban-daban na duniya Karo na Goma sha Ɗaya, (11) wanda aka gudanar a ɗakin taro na Jama'ar maryam Abacha Amerikan University da ke Kano.
Sannan har wala yau ya kuma bayyana Farfesa Gwarzo da cewa mutum ne mai karamci, domin ya karrama su kuma sun gani a aikace.
Ya ce, "ya karrama mu ya mutunta mu, duk abin da ake yi wa baƙo a faranta masa, ya yi mana. Kuma tsare-tsaren da aka yi, babu bambanci da cewa taron da aka yi a Abuja ne aka yi shi".
Ya ce za su riƙa kai taron rantsar da ɗalibai sassa daban-daban na ƙasar nan, kuma yadda suka ga taron na bana a Jami'ar Maryam Abacha American University, sun yaba matuƙa.
Ya kuma yi kira ga É—aliban da su ji tsoron Allah, ya ce, "aikin nan da kuka yi karatu domin shi ku gudanar da shi ta yadda su al'umma za su bambance ma'aikacin jinya da wanda ba na jinya ba.
"Amfanin ilimi ka kawo canji. Al'umma na da Æ™orafi ga ma'aikatan jinya, ilimi shi zai kawo canji. Ku yi amfani da wannan basirar ilimin da kuka samu domin kawo canji ga al'umma kan matsayin yadda suke yi wa ma’aikatan jinya kallo."
Dr. Faruq ya ce akwai buƙatar ɗaliban su sauya tunanin al'umma domin su fahimci cewa aikin jinya aiki ne na ƙwarai da kuma taimakon al'umma da kawo ci gaba ga mara lafiya.
No comments