Daga Musa Muhammad Gwamnan jihar Zamfara, Dauda Lawal ya yi alƙawarin bayar da cikakken goyon bayan sa ɗari bisa ɗari ga Hukumar yaƙi da sha...
Daga Musa Muhammad
Gwamnan jihar Zamfara, Dauda Lawal ya yi alƙawarin bayar da cikakken goyon bayan sa ɗari bisa ɗari ga Hukumar yaƙi da shan miyagun ƙwayoyi ta NDLEA don kawar da abin a duk faɗin jihar.
Gwamnan ya bayyana haka ne a lokacin da ya karɓi baƙuncin Kwamandan Hukumar ta NDLEA na jihar a ofishin sa, a wata ziyara da ya kai fadar gwamnatin jihar yau Talata.
Kamar yadda ya ke ƙunshe cikin wata sanarwa da mai magana da yawun Gwamnan, Sulaiman Bala Idris ya sanya wa hannu, Kwamandan ya bayyana wasu matsaloli da su ke fuskanta a wannan yaƙi da su ke yi a jihar.
Da ya ke mayar da jawabi, Gwamna Lawal ya tabbatar wa da Kwamandan shirin sa wajen haɗa hannu da Hukumar don kawar da wannan muguwar ɗabi'a a duk faɗin jihar.
Gwamnan ya ce "Gwamnatin jiha na da buƙatar samun fahimtar juna da Hukumar NDLEA wajen shawo kan mummunar ɗabi'ar shaye-shaye, za kuma mu bayar da matuƙar goyon bayan mu wajen ganin an daƙile shigo da miyagun ƙwayoyi cikin jihar nan."
Haka kuma Gwamnan ya ta'allaƙa taɓarɓarewar harkar tsaron da jihar ke fama da shi ga yawan shaye-shayen da ake fama da su, "domin yawancin waɗannan 'yan bindiga su na aiwatar da ta'asar su ne sakamakon shaye-shayen. Haƙƙin mu ne mu samar da maganin wannan matsala," in ji Gwamnan.
Don haka Gwamnan ya yi alƙawarin sake gyara cibiyar kula da lalurar ƙwaƙwalwa da ke Gusau da samar da gidajen kwana da ofisoshi ga Hukamar ta NDLEA, tare da samar masu da motoci don su ji daɗin aiki.
Tun farko cikin jawabinsa, Kwamandan Hukumar na jihar, Bamidele Amos Segun, ya bayyana wa Gwamnan irin gudumawar da Hukumar ta ke bayarwa wajen daƙile sha da shigo da miyagun ƙwayoyi a jihar.
Ya ce, "ina matuƙar farin ciki da kasancewa tare da kai a yau, tare da miƙa godiya ga Allah da ya azurta Zamfara da mutum irin ka."
Kwamandan ya ci gaba da bayyana cewa, "bisa abubuwan da muka lura da su, Zamfara na samun ci gaba wajen dawowar ta kan turba a ƙarƙashin mulƙin ka. Mu a NDLEA muna tabbatar maka da cikakken goyon bayan mu wajen ganin an daƙile wannan harka da shaye-shaye a duk faɗin jihar."

No comments