Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Gwamanti na za ta samar da harkar shari'a mai cin gashin kan ta - Dauda Lawal

Daga Musa Muhammad Gwamnan jihar Zamfara, Dauda Lawal ya jaddada aniyar sa ta tabbatar da samar da harkar shari'a mai cin gashin kan ta...



Daga Musa Muhammad

Gwamnan jihar Zamfara, Dauda Lawal ya jaddada aniyar sa ta tabbatar da samar da harkar shari'a mai cin gashin kan ta, mai cikakken iko a jihar. 

Gwamnan ya yi nuni da haka ne a lokacin da ya kai ziyarar gani da ido a manyan kotunan jihar a ranar Litinin da ta gabata, inda ya fara da rukunin ma'aikatar shari'a ta jihar da ke Gusau. 

Cikin wata sanarwa da Kakakin Gwamnan, Sulaiman Bala Idris ya sanya wa hannu, ta bayyana cewa maÆ™asudin wannan ziyara dai shi, don Gwamnan ya gane wa idanunsa halin da kayan aiki su ke ciki a manyan kotunan jihar. 

Idris ya ƙara da cewa Babbar Jojin jihar, Mai shari'a Kulu Aliyu ce ta tarbi Gwamnan, in da ta yi masa cikakken bayanin halin da kotunan ke ciki, tare da bayyana masa abubuwan da su ke buƙata daga gwamnati.

Takardar sanarwar ta Sulaiman Bala ta bayyana cewa, cikin jawabin Gwamna Dauda, ya bayyana aniyar gwamnatin sa ta gani ya bayar da duk wata gudawar da wannan harka ta shari'a ke buƙata.

Daga nan Gwamnan ya yi alÆ™warin cewa gwamnatin sa ba za ta rinÆ™a tsoma bakin ta a harkar shari'ar ba, tare da bayar da tabbacin kula da haƙƙoÆ™in AlÆ™alai, waÉ—anda suka haÉ—a da gidajen su da kuma gyaran ofisoshin su. 

Gwamna Dauda Lawal ya kuma bayyana harkar Shari'a a matsayin ita ce kaÉ—ai hanyar da mai Æ™aramin Æ™arfin ke samun madogara. 

Don haka ya bayyana irin jajircewar gwamnatin sa wajen harkar shari'a mai Æ™arfi kuma mai ci kakken iko, tare da nuni da cewa a matsayin harkar shari'a na wani reshe mai muhimmanci a gwamnati, za a ba ta damar gudanar da ayyukan ta yadda ya dace. 

Tun farko a cikin jawabinta, Babbar Jojin jihar, Mai shari'a Kulu Aliyu ta yaba wa Gwamnan ne bisa irin kulawar da ya ke ba ma'aikatar shari'ar, "muna matuƙar godiya da duk irin abubuwan da ka ke yi mana. Duk lokacin da mu ka nemi wata gudumawa daga gare ka, ba ka gajiyawa wajen biya mana ita," in ji Ba bbar Jojin jihar.

No comments