Rundunar dakarun tsaro masu sanye da kayan karki na RSF a Sudan ta ƙwace iko da birnin Nyala, birni na biyu mafi girma a ƙasar . RSF ta ƙwac...
Rundunar dakarun tsaro masu sanye da kayan karki na RSF a Sudan ta ƙwace iko da birnin Nyala, birni na biyu mafi girma a ƙasar .
RSF ta ƙwace iko da birnin daga hannun dakarun sojin ƙasar bayan shafe watanni ana gwabza yaƙi, kamar yadda wasu majiyoyi suka shaida wa BBC.
Wani shaida a yankin ya ce mazauna birnin na cike da murna, saboda suna fatan hakan zai kawo ƙarshen rikicin yankin.
Rikicin ya tilasta wa fiye da mutum 670,000 barin gidajensu.
An lalata asibitocin birnin, inda rohotonni ke cewa an yi ta ganin gawarwaki zube a kan titunan birnin.
Ƙwace birnin da RSF suka yi na zawa ne, yayin da ɓangarorin da ke faɗa da juna ke shirin komawa teburin sulhu a ƙasar Saudiyya.
Kawo yanzu rundunar sojin ƙasar ba ta ce komai ba game da cin galabarta a birnin Nyala.
Nyala - wanda shi ne babban birnin jihar Darfur ta Kudu - shi ne birnin da ke kan iyakar Sudan da ƙasar Jamhuriyar tsakiyar Afirka.
RSF ta samo asali ne daga Darfur, inda aka zarge ta da laifukan cin zarafin ƙungiyoyin da ba na Larabawa ba a yankin, lokacin yaƙin na wannan yaƙin.
A 'yan makonnin da suka gabata ne aka kashe manyan sojoji a birnin ciki har da shugaban rundunar sojin ƙasar a birnin.

No comments