Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

An zaɓi Sultan Ibrahim a matsayin sabon sarkin Malesiya

Malaysia ta zaɓi Sultan Ibrahim na jihar Johor da ke kudancin ƙasar a matsayin sabon sarkinta. Sarakunan ƙasar tara ne suka zaɓi Sultan Ibra...



Malaysia ta zaɓi Sultan Ibrahim na jihar Johor da ke kudancin ƙasar a matsayin sabon sarkinta.

Sarakunan ƙasar tara ne suka zaɓi Sultan Ibrahim a taron sarakunan ƙasar da aka yi ranar Juma’a kuma za a naɗa shi a ranar 31 ga watan Janairu na shekara mai zuwa.

Sultan Ibrahim ya yi fice da bayyana ra’ayinsa kan siyasa kuma yana da kyakkyawar alaƙa da Firaminista Anwar Ibrahim.

Bugu da ƙari, yana jagorantar wasu dakaru masu zaman kansu kuma ɗan kasuwa ne a ɓangaren gine-gine da ma'adanai

An zaɓi sarkin - wanda shi ne shugaban ƙasa a tsarin dimokuraɗiyyar majalisar dokokin Malaysia - a cikin wani tsari na musamman da shugabannin iyalan gidan sarautar ƙasar waɗanda ke kan gaba wajen zama sarki na tsawon shekaru biyar.

No comments