Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Shugaba Tinubu Zai Gabatar Da Jawabin Ranar ’Yancin Kai Ta Nijeriya A gtobe Alhamis

Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu zai yi wa ’yan Nijeriya jawabi a ranar Alhamis, 1 ga Oktoba, 2026, domin bikin cika shekaru 66 da samun ’yan...

Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu zai yi wa ’yan Nijeriya jawabi a ranar Alhamis, 1 ga Oktoba, 2026, domin bikin cika shekaru 66 da samun ’yancin kan Nijeriya. Jawabin shugaban ƙasar zai gudana ne da ƙarfe 7:00 na safe, kamar yadda Fadar Shugaban Ƙasa ta sanar.

Sanarwar da mai ba shugaban ƙasa shawara kan yaɗa labarai da dabaru, Bayo Onanuga, ya fitar a ranar 30 ga Satumba, 2026, ta ce za a watsa jawabin ga ’yan Nijeriya ta gidajen talabijin da gidajen rediyo da sauran kafafen yaɗa labarai.

Fadar Shugaban Ƙasar ta buƙaci dukkan gidajen talabijin da rediyo da sauran kafafen yaɗa labarai da su haɗa kai da shirye-shiryen watsa labarai na gidan talabijin na ƙasa, NTA, da Hukumar Gidajen Rediyon Tarayya, FRCN, domin isar da jawabin ga al’umma.

Nijeriya na bikin cika shekaru 66 da samun ’yancin kai daga Birtaniya a ranar 1 ga Oktoba, 2026. Ana gudanar da bikin ne domin tunawa da samun ’yancin ƙasar a shekarar 1960, tare da yin nazari kan tafiyar ƙasa da ƙalubalen da take fuskanta wajen ci gaba da gina haɗin kai da wadata.
 

No comments