Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Kamfanonin Sadarwa Sun Goyi Bayan Umarnin CBN Kan Ajiyar Bayanai A Cikin Ƙasa

Ƙungiyar Masu Lasisin Ayyukan Sadarwa ta Nijeriya (ALTON) ta jaddada goyon bayan ta ga umarnin Babban Bankin Nijeriya (CBN) da ke tilasta wa...

Ƙungiyar Masu Lasisin Ayyukan Sadarwa ta Nijeriya (ALTON) ta jaddada goyon bayan ta ga umarnin Babban Bankin Nijeriya (CBN) da ke tilasta wa bankuna, kamfanonin fintech, da sauran masu hidimar biyan kuɗi su riƙa adana bayanan mu’amalar kuɗi a cikin Nijeriya.

Shugaban ALTON, Gbenga Adebayo, ya ce wannan mataki zai ƙarfafa ikon Nijeriya wajen sarrafa bayanan dijital da kuma inganta tsaron muhimman bayanan kuɗi.

Umarnin CBN, wanda zai fara aiki daga ranar 1 ga Janairu, 2027, ya tanadi cewa duk bayanan ma’amalar biyan kuɗi da aka samar a Nijeriya dole ne a ajiye su a kan rumbun ajiyar bayanai (servers) da ke cikin ƙasar nan, a matsayin wani ɓangare na ƙoƙarin ƙara sa ido kan tsarin biyan kuɗi na dijital da ke ci gaba da bunƙasa.

Adebayo ya bayyana cewa haƙƙin mallakar ikon bayanai yana nufin ƙasa ta ɗauki alhakin dukkanin tsarin bayanai, tun daga tattarawa, sarrafawa, adanawa, har zuwa tabbatar da kariya da ingancin su.

Ya ce: “Ba za mu ci gaba da miƙa bayanan mu ga wasu ƙasashe ba. Yayin da muke ƙara adana bayanan mu a cikin ƙasa, hakan zai fi mana amfani.”

Ya bayyana cewa adana bayanai a cikin Nijeriya zai rage jinkiri wajen gudanar da mu’amala, ya rage kuɗin dawo da bayanai, sannan ya inganta aiki saboda ba za a dogara sosai da rumbun ajiyar bayanai da ke ƙasashen waje ba.

A cewar sa, idan ana ajiye bayanai a ƙasashen waje, duk lokacin da ake buƙatar samun bayanai sai sadarwa ta ratsa iyakokin ƙasa, wanda hakan ke ƙara jinkiri da kuma ƙarin kuɗaɗe.

Shugaban na ALTON ya bayyana wannan manufar a matsayin muhimmin mataki na farko wajen cimma burin Nijeriya na mallakar cikakken ikon bayanan ta.

Ya ce Nijeriya na da isasshen ƙarfin fasahar adana bayanai, inda ya ƙara da cewa yanzu haka har ma wasu cibiyoyin adana bayanai mallakar ‘yan Nijeriya suna karɓar bayanan ƙungiyoyi daga wasu ƙasashe.

Ya ce: “Idan mutane daga ƙasashen waje za su iya ajiye bayanan su a nan, me ya sa mu ba za mu iya ajiye namu a nan ba?”

Adebayo ya yi watsi da damuwar da wasu ke nunawa kan tsaro da amincin tsarin, yana mai cewa masu kula da bayanan cikin gida suna da kishi da shauƙin kare bayanan Najeriya.

Ya ce: “Babu wanda zai iya kare gidan ka fiye da kai kan ka.”
Ya kuma bayyana cewa ajiyar bayanai a cikin ƙasa zai taimaka wajen rage dogaro da kayan aiki daga ƙasashen waje, tare da rage matsin canjin kuɗi, domin kamfanoni za su riƙa biyan kuɗin hidima da naira maimakon kuɗin waje.

Adebayo ya bayyana cewa a halin yanzu Nijeriya tana da kusan cibiyoyin adana bayanai na matakin 'Tier III" guda shida, sannan akwai wasu sabbi da ake ginawa.

Sai dai ya jaddada cewa abin da ya fi muhimmanci ba yawan cibiyoyin ba ne, sai dai ƙarfin abin da za su iya ɗauka.

Ya ce, “Ba wai yawan su kawai ake dubawa ba; abin da ya fi muhimmanci shi ne ƙarfin bayanan da za su iya karɓa. Kuma a yanzu muna da wannan ƙarfin.”

Ya ƙarfafa masu ruwa da tsaki da su gaggauta ƙara mayar da tsarin adana da sarrafa bayanai cikin gida, yana mai cewa mallakar ikon bayanan ƙasa zai taimaka wajen bunƙasa tattalin arzikin dijital na Nijeriya.
 

No comments