Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Nijeriya Na Nan Daram, Tana Samun Ci Gaba Mai Ɗorewa – Ministan Yaɗa Labarai

Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, ya yi watsi da iƙirarin da ake yi na cewa wai Nijeriya na daf da rugujewa, yan...


Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, ya yi watsi da iƙirarin da ake yi na cewa wai Nijeriya na daf da rugujewa, yana mai jaddada cewa ƙasar tana nan daram kuma tana samun ci gaba mai ɗorewa.

Idris ya bayyana hakan ne a ranar Laraba a Abuja, a lokacin Babban Taron Ƙasa na 81 da Taron Shekara-shekara na 23 na Ƙungiyar Masu Watsa Labarai ta Nijeriya (BON).

Ya ce: “Ba gaskiya ba ne cewa Nijeriya na daf da rugujewa. A maimakon haka, muna ci gaba da nuna juriya tare da ɗaukar matakai masu ƙarfi wajen tunkarar matsalolin tsaro da tattalin arziki.”

Dangane da tsaro, Ministan ya ce cigaba da kai samamen soji da kuma inganta haɗin gwiwa a ɓangaren bayanan sirri suna samar da sakamako mai kyau, inda ya buga misali da samamen baya-bayan nan a jihohin Zamfara da Neja, inda jami’an tsaro suka ragargaji ‘yan bindiga tare da daƙile hare-haren da suka shirya kaiwa.

Ya ƙara da cewa: “Haɗin gwiwar sojoji da sauran jami’an tsaro ya samar da gagarumar nasara a sassa daban-daban na ƙasar nan, kuma muna ƙara ƙarfafa tsarin tattara bayanan sirri da saurin kai ɗauki domin kare rayuka da dukiyoyi.”

Game da tattalin arziki, Idris ya ce alamu suna nuna farfaɗowa da ƙaruwar amincewar masu zuba jari, ya ƙara da cewa gyare-gyaren da ake yi a ɓangarorin man fetur da sauran fannoni suna taimakawa wajen faɗaɗa hanyoyin samun kuɗaɗen shiga da kuma daidaita asusun gwamnati.

Ya ce: “Ajiye kuɗaɗen ƙasashen waje yana ƙaruwa, amincewar masu zuba jari tana ƙaruwa, kuma gyare-gyaren da ake yi a ɓangarorin mai da waɗanda ba na mai ba suna faɗaɗa hanyoyin samun kuɗaɗen shiga.”

Ministan ya kuma ambaci dawo da Nijeriya matsayin "Frontier Market" da kamfanin FTSE Russell ya bayyana a matsayin wata alama ta ƙara amincewar duniya da tattalin arzikin ƙasar nan.

Bugu da ƙari ya buƙaci kafafen yaɗa labarai da su kiyaye ƙa’idojin aiki da kuma tabbatar da sahihancin rahotanni, musamman yayin da ƙasar nan take tunkarar wani sabon zagayen zaɓe, yana mai jaddada muhimmancin rawar da suke takawa wajen tsara fahimtar jama’a da kuma inganta haɗin kan ƙasa.

Ya ce: “Dole ne kafafen yaɗa labarai su ci gaba da sanarwa, ilimantarwa da haɗa kan jama’a, tare da bin ƙa’idojin ƙwarewa, adalci da sahihanci a aikin su.”

Idris ya jaddada ƙudirin Gwamnatin Tarayya na tallafa wa kafafen yaɗa labarai, yana mai kira da a ƙarfafa haɗin gwiwa domin yaƙar labaran ƙarya da kuma ƙarfafa haɗin kan ƙasa.

Ya yaba wa Ƙungiyar Masu Watsa Labarai ta Nijeriya bisa rawar da take takawa wajen inganta ƙwarewa a fannin, sannan ya ayyana buɗe babban taron BON karo na 81, yana mai bayyana fatan cewa za a samar da hanyoyin warware matsalolin da fannin ke fuskanta.

Daga cikin waɗanda suka halarci taron akwai Shugaban Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kan ta (INEC), Farfesa Joash Amupitan; Darakta-Janar na Hukumar Kula da Watsa Labarai ta Ƙasa (NBC), Dakta Charles Ebuebu; Darakta-Janar na Gidan Talbijin ta Nijeriya (NTA), Salihu Abdulhamid Dembos; Darakta-Janar na Hukumar Tace Tallace-Tallace ta Nijeriya (ARCON), Mista Olalekan Fadolapo; Darakta-Janar na gidan rediyon Muryar Nijeriya (VON), Malam Jibrin Baba Ndace; Darakta-Janar na FRCN, Mohammed Bulama, da sauran su.


 

No comments