Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya isa birnin Abu Dhabi na ƙasar Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa (UAE) a daren Lahadi, domin halartar taron Abu D...
Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya isa birnin Abu Dhabi na ƙasar Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa (UAE) a daren Lahadi, domin halartar taron Abu Dhabi Sustainability Week (ADSW) na 2026, wanda zai fara a yau Litinin.
Jirgin Shugaban Ƙasan ya sauka a Sashen Shugaban Ƙasa na Filin Jirgin Sama na Zayed da misalin ƙarfe 11:30 na dare agogon Dubai. Ministan Harkokin Wajen UAE, Sheikh Shakhboot Nahyan Al Nahyan, tare da Jakadan UAE a Nijeriya, Salem Saeed Al-Shamsi, da Ministan Harkokin Wajen Nijeriya, Amb. Yusuf Maitama Tuggar, da kuma jami’an ofishin jakadancin Nijeriya a Abu Dhabi ne suka tarbe shi.
Haka kuma, wasu ministoci da suka haɗa da Ministan Kasafi da Tsare-tsare, Atiku Bagudu, Ministan Masana’antu, Ciniki da Zuba Jari, Dr. Jumoke Oduwole, da Darakta-Janar na Hukumar Leken Asiri ta Ƙasa (NIA), Amb. Muhammed Muhammed, sun tarbe Shugaban Ƙasan a otal ɗinsa.
Kafin isowarsa Abu Dhabi, Shugaba Tinubu ya shafe wani ɓangare na hutun ƙarshen shekara a Turai, inda ya yi muhimman tattaunawa da Shugaban Rwanda, Paul Kagame, da Shugaban Faransa, Emmanuel Macron.
Taron ADSW 2026, mai taken “The Nexus of Next, All Systems Go”, dandali ne na duniya da ke haɗa shugabanni, masu tsara manufofi, masu zuba jari da ƙwararru domin tattaunawa da ɗaukar matakai kan ci gaba mai dorewa, yaƙi da sauyin yanayi, sauya tsarin makamashi da bunƙasa tattalin arziki da ya haɗa kowa da kowa.
Ziyarar ta ƙara jaddada kyakkyawar alaƙar diflomasiyya da tattalin arziki tsakanin Najeriya da UAE, tare da nuna matsayar Najeriya a matsayin ƙasa mai taka rawa a tattaunawar duniya kan ci gaba mai dorewa.


No comments