Hukumar Asusun kula da yara ƙananan yara ta majalisar ɗinkin duniya (UNICEF) ta jinjina wa gwamnatin jihar Kaduna bisa zama jihar farko a Ni...
Hukumar Asusun kula da yara ƙananan yara ta majalisar ɗinkin duniya (UNICEF) ta jinjina wa gwamnatin jihar Kaduna bisa zama jihar farko a Nijeriya da ta amince, kuma fara aiwatar da shirin samar da abinci mai gina jiki da lafiya ga yara ƙanana (RUTF), wanda hakan ya zama wani muhimmin mataki wajen yaƙar ƙarancin abinci mai gina jiki tsakanin yara.Da ta ke jawabi yayin wani taron haɗin gwiwa da gwamnatin jihar Kaduna, wakiliyar UNICEF a Nijeriya, Wafaa Saeed Abdelatef, ta bayyana yadda jihar Kaduna ta nuna gagarumar jajircewa a bangaren kiwon lafiya tare da samar da walwalar yara da cika alƙawuran kuɗin haɗin gwiwa akai-akai.
Ta ce, “Jihar Kaduna ta zama abin koyi ga sauran jihohi, bisa yadda gwamnati ta rungumi shirin samar da abinci mai gina jiki da lafiya ( RUTF) da sauri, kuma ta fara aiwatar da shi na nuna cikakkiyar niyya wajen kare rayuwar yara da tabbatar da cewa babu wani yaro da zai ci gaba da fama da rashin abinci mai gina jiki,”
Taron wanda aka gudanar da shi a fadar gwamnatin jihar Kaduna, ya zama abin tarihi a dangantakar haɗin gwiwar da ke tsakanin UNICEF da gwamnatin jihar Kaduna wajen inganta lafiya da walwalar yara.
Gwamna Uba Sani ya tabbatar da cewa gwamnatin sa za ta ci gaba da gini kan wannan nasara, inda ya bayyana shirin RUTF a matsayin wani muhimmin ɓangare na dabarar gwamnatin sa wajen yakar rashin abinci mai gina jiki da inganta ci gaban jama’a baki ɗaya.
“Ƙaddamar da rabon abincin RUTF a faɗin jihar Kaduna wani babban mataki ne na kawo ƙarshen cutar ƙarancin abinci mai gina jiki,”
“Mun ƙuduri aniyar cewa babu wani yaro da za a bar shi a baya wajen yaƙar yunwa, rashin lafiya, da kuma samar da makoma mai kyau.” in ji gwamna Uba Sani.
Gwamnan ya kuma gode wa UNICEF bisa wannan haɗin gwiwar da ke samar da sauye-sauye masu amfani a fannoni kamar su lafiya, abinci mai gina jiki, ilimi, da tsaftar ruwa da muhalli.
Ya ƙarƙare da cewa shiga jihar Kaduna cikin muhimman shirye-shirye irin su RUTF da ASWA III wanda Kaduna ita kaɗai ce ta shiga cikin sa a Nijeriya na nuna hangen nesan gwamnatinsa na gina tsarin da ke tallafa wa marasa ƙarfi a fadin jihar baki ɗaya.

No comments