Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Gwamna Uba Sani Ya Amince Da Ɗaukar Jami'an Lafiya 1,800 A Kaduna

Gwamnatin Jihar Kaduna ta sanar da shirin ɗaukar ƙarin ma’aikatan lafiya 9,000 a cikin shekaru biyar masu zuwa domin ƙarfafa harkar lafiya a...



Gwamnatin Jihar Kaduna ta sanar da shirin ɗaukar ƙarin ma’aikatan lafiya 9,000 a cikin shekaru biyar masu zuwa domin ƙarfafa harkar lafiya a faɗin jihar.

Kwamishinan Yaɗa Labarai na jihar, Ahmad Maiyaki, ne ya bayyana haka a ranar Lahadi a Kaduna, yayin wani taron tattaunawa da kafafen yaɗa labarai da Hukumar Inshorar Lafiya ta Kaduna (KADCHMA) ta shirya tare da haɗin gwiwar ƙungiyar lafiya ta “Lafiya: UK–Nigeria Partnership for a Healthier Future.”

A cewarsa, Gwamna Uba Sani ya amince da ɗaukar ma’aikatan lafiya 1,800 nan take a matakai daban-daban, kuma wannan mataki zai ci gaba a kowace shekara cikin shekaru biyar masu zuwa har zuwa cika adadin 9,000.

Maiyaki ya ce gwamnatin Sani ta ɗauki bangaren lafiya a matsayin haƙƙin kowa, ba kawai fifiko ba, domin tabbatar da cewa kowane ɗan jihar na samun damar kulawa da lafiya.

“Gwamna Sani ya sanya bangaren lafiya a gaba tun daga shekarar 2023 zuwa yau. Ba wai kawai ya ɗauki lafiya a matsayin fifiko ba, har ma yana kallonta a matsayin haƙƙin kowane ɗan jihar Kaduna,” inji shi.

Kwamishinan ya ƙara da cewa gwamnatin jihar ta ƙara kaso mai tsoka ga kasafin kuɗin lafiya — sama da matsakaicin kaso na ƙasa (15%) — domin tabbatar da cewa an samu isassun kayan aiki da ma’aikata a cibiyoyin lafiya.

Ya kuma bayyana cewa gwamnati ta inganta albashin ma’aikatan lafiya, wanda hakan ya ja hankalin likitoci da sauran ma’aikata su koma aikin gwamnati a jihar.

“Yanzu likitoci da sauran ma’aikatan lafiya suna komawa Kaduna domin aiki, saboda an inganta albashi da walwala. A yau, Kaduna ce ke kan gaba daga cikin jihohin Arewa 19 wajen inganta harkar lafiya,” inji Maiyaki.

Ya kuma yi kira ga ‘yan jarida da su ci gaba da tallafawa shirye-shiryen gwamnati ta hanyar wayar da kan jama’a kan muhimmancin neman kula da lafiya da wuri.

Wannan shirin dai na daga cikin dabarun gwamnatin Uba Sani na cimma Universal Health Coverage (UHC), wato tsarin da ke nufin tabbatar da cewa kowa na samun kulawar lafiya mai inganci ba tare da wahalar kuɗi ba.

No comments