Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Yadda Gwamnatin Uba Sani Ke Inganta Harkokin Kiwon Lafiya A Faɗin Jihar Kaduna

A ƙoƙarin sa na samar da  jagorancin sahihi ga ɗaukacin a'lumma, Gwamna Uba Sani na ci gaba da samun gagarumin ci gaba a fannin kiwon la...


A ƙoƙarin sa na samar da  jagorancin sahihi ga ɗaukacin a'lumma, Gwamna Uba Sani na ci gaba da samun gagarumin ci gaba a fannin kiwon lafiya, wanda ke ƙara tabbatar da ƙudirin sa na samar da ingantacciyar rayuwa ga al’ummar jihar Kaduna.

Tun daga hawan sa kan mulki a shekarar 2023, Gwamna Uba Sani ya ɗauki kiwon lafiya a matsayin ɗaya daga cikin manyan ababen da ya fi bai wa fifiko a ƙudirorin sa na  mulki.

Gina Sabbin Asibitoci da Gyaran Tsofaffi: 

Gwamnatin Gwamna Uba Sani ta fara da gina sabbin cibiyoyin kiwon lafiya a kananan hukumomi da dama, musamman a yankunan karkara da ke fama da rashin isassun wuraren jinya. Baya ga haka, an gyara wasu tsofaffin asibitoci da suka dade suna bukatar kulawa, inda aka sabunta kayan aikin likitoci tare da horas da ma’aikatan lafiya.

Karin Ma’aikatan Lafiya da Koyar da Sabbin Fasahohi: 

Wani muhimmin ci gaba shi ne daukar sabbin ma’aikatan lafiya – ciki har da likitoci, nas-nas da masu jinya – domin cike gibin da ke akwai a fannin. Bugu da kari, gwamnati ta kaddamar da shirye-shiryen horaswa don sabunta ilimi da kwarewar ma’aikatan lafiya, musamman kan sabbin hanyoyin bincike da magani.

Tallafa wa Marasa Galihu da Kaddamar da Shirin Kiwon Lafiyar Iyali: 

Gwamnatin Kaduna ta kaddamar da shirin kiwon lafiyar iyali wanda ke bai wa mata da yara damar samun kyauta ko rangwamen jinya a asibitocin gwamnati. Wannan ya rage wa talakawa radadin kashe kudade wajen neman lafiya, kuma ya karfafa gwiwar mutane su rika zuwa asibiti da wuri.

Fadada Shirin Inshorar Lafiya na Jihar (KADCHMA): 

A karkashin jagorancin Gwamna Uba Sani, an fadada shirin inshorar lafiya na jihar Kaduna (KADCHMA) domin ya rika kunshe da karin mutane, musamman ma’aikata da marasa galihu. Wannan shiri yana taimaka wa mutane samun magani ba tare da sai sun biya kudi da hannu ba.

Gwamna Uba Sani ya nuna cewa inganta fannin kiwon lafiya ba kawai aiki ba ne, illa wajibi ne ga kowace gwamnati mai kishin jama’a. A yau, al’ummar Kaduna na ci gaba da amfana da sauye-sauyen da aka samu a bangaren lafiya, wanda hakan ke ba da fata da kwarin gwiwa cewa zaman lafiya da jin dadin jama’a na samuwa a hankali.

No comments