Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Yadda Shugaba Tinubu Ya Kai Ziyarar Ta'aziyyar Marigayi Aminu Ɗantata

Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya kai ziyarar ta’aziyya a Kano, inda ya bayyana marigayi Alhaji Aminu Ɗantata a matsayin gwarzo, mutumin ki...


Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya kai ziyarar ta’aziyya a Kano, inda ya bayyana marigayi Alhaji Aminu Ɗantata a matsayin gwarzo, mutumin kirki, jajirtacce, mai sadaukar da kai wajen jin ƙai da tallafa wa al’umma.

Shugaban ya ce rayuwar Alhaji Ɗantata cike take da yawan ibada, hidima, da ɗabi’un kirki waɗanda suka kasance abin koyi ga kowa.

Marigayi Ɗantata ya rasu ne a Dubai ranar Asabar, 28 ga Yuni, 2025 yana da shekaru 94, kuma an yi jana’izar sa a Madina a ranar Talata 1 ga Yuli.

Shugaba Tinubu ya bayyana ziyarar a matsayin ta musamman, yana mai cewa Ɗantata ba wai babban mutum ne kawai a kasuwanci ba, ɗan gida ne a wurin sa. Ya kuma tuna yadda ya nemi addu’o’in sa kafin zaɓen 2023.

Cikin jawabin sa na maraba, Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya nuna godiya ga Shugaban Ƙasa bisa jajantawa da goyon bayan da ya bai wa iyalan marigayin da kuma al’ummar jihar.

Ya ce bayan rasuwar Ɗantata, Shugaban Ƙasa ya tura tawagar gwamnatin tarayya zuwa Saudiyya ƙarƙashin jagorancin Ministan Tsaro, sannan ya sake turo Mataimakin Shugaban Ƙasa da wasu Ministoci domin ta’aziyya, kafin daga bisani ya je da kansa duk da tarin aikin sa.

A jawabin sa, ɗan marigayin, Alhaji Tajudeen Aminu Ɗantata, ya nuna matuƙar godiya ga Shugaban Ƙasa bisa wannan karamci da karramawa da ya nuna. Ya tabbatar da cewa za su ci gaba da riƙe ƙimomin da mahaifin su ya bari.

Wannan ta’aziyyar ylta samu halartar manyan jami’an gwamnati, ciki har da Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Godswill Akpabio, Mataimakin sa Sanata Barau Jibrin, Gwamnan Jigawa, da attajirai irin su Alhaji Aliko Ɗangote da Alhaji Mohammed Indimi.
 

No comments