Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

TIBETAN SKY: Ƙabilar Da Su Ke Bai Wa Ungulu Gawar ’Yan Uwan Su

Al’ada wata abu ce da ƙabilu da yawa suka ɗauke ta da muhimmanci wasu ma kamar addini haka suka mayar da abin. Yanzu kusan kowacce ƙabila su...


Al’ada wata abu ce da ƙabilu da yawa suka ɗauke ta da muhimmanci wasu ma kamar addini haka suka mayar da abin.

Yanzu kusan kowacce ƙabila su na da al’adar da su ke gabatarwa wanda suka taso su na yi tun iyaye da kakanni, wasu al’adun gwanin birgewa wasu kuma sai a hankali domin abinda suke gabatarwa cikin ƙabilar tasu a matsayin al’ada kwata-kwata sai a hankali.

Misali kamar al’adar da za ace mata idan sukai ciki baza su haihu a garin ba saidai a fitar dasu daji su haihu a can. Ko kuma ƙabilar da maza biyu ne ke auren mace ɗaya. Da dai sauran abubuwa.

Amma a yau za mu kawo muku wata ƙabila da ba sa binne ’yan uwansu, sai dai su kaiwa ungulu su cinye gawar.

Kamar yadda kowa dai ya riga ya sani a addinai guda biyu da muke da shi Musulunci da kuma addinin Kirista duk wani mutum da ya mutu binne gawarsa ake yi.

To saidai su a wannan ƙabilar ta Tibetan sky cikin addinin Buddhism ko kuma mu ce addinin Budda su idan ɗan uwansu ya mutu ba sa binne shi sai dai su samu wani farin kyalle su rufe gawar su ɗauke ta su kai can kwanar ƙofar gidansu ajiye zuwa kwana uku ko kwana biyar.

Dangin wanda ya mutum sukan daina aikata komai saidai su share ko ina su tabbatar babu datti a wurin wai domin ruhin mamacin ya samu gurin zama mai kyau.

Iyalan mamacin bayan sun yi hakan sai su zaɓi rana ɗaya wacce suke ganin tafi sauran ranaku daraja sai su ɗauke wannan mamacin su kai shi can wani wuri kusa da wasu duwatsu su zaunar da gawar su zora kan gawar bisa gwiwarsa.

Daga nan sai su tafi su barwa ungulun da suke gurin su zo su cinye naman gawar.

Da zarar sun cinye shekenan sai ’yan uwan mamacin su tafi suna farin ciki wai ɗan uwansu ya tafi babu wani zunubi a kansa.

No comments