Mataimakin shugaban Nijeriya, Sanata Kashim Shettima, ya bayyana matuƙar kaɗuwar sa da rasuwar tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari, inda y...
Mataimakin shugaban Nijeriya, Sanata Kashim Shettima, ya bayyana matuƙar kaɗuwar sa da rasuwar tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari, inda ya bayyana ranar a matsayin baƙar rana ga duk ɗan Nijeriya.
A cikin saƙon ta’aziyyar da ya aike wa manema labarai a ranar Lahadi, Shettima ya ce Nijeriya ta rasa kataɓus sakamako babbar asarar da ta tafka na rashin tsohon shugaban Muhammadu Buhari
"Zuciyata ta cika da alhini da jimami, yayin da al'ummar kasar ke zaman makokin daya daga cikin manyan shugabannin da ba kasafai zamani ke iya samar da su ba irin mai girma tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari, GCFR," in ji Shettima.
Mataimakin shugaban kasar wanda a kwanakin baya ya ziyarci Buhari a wani asibiti a kasar Birtaniya, ya ce ya sa ran tsohon shugaban kasar zai sami sauki cikin gaggawa ya dawo gida. Inda yake cewa "Wannan rashi ya yi muni matuka fiye da yadda baki zai iya bayyanawa, labarin mutuwar ya zo min a daidai lokacin da nake masa tsammanin murmurewa cikin sauri bayan da na ziyarce shi a asibiti a Burtaniya," in ji shi.
Mataimakin shugaban kasar ya mika ta'aziyya ga iyalan Buhari, da gwamnati da al'ummar jihar Katsina, da gwamnatin Najeriya da 'yan Najeriya. Inda yayi musu fatan samin dangana da fatan ƙasar za ta rike kyawawan koyarwar marigayi Buhari
No comments