Aƙalla Falasɗinawa 32 Isra'ila ta kashe lokacin da suke kan layin karɓar kayan abinci a kusa da cibiiyoyi biyu ranar Asabar a Zirin Gaza...
Aƙalla Falasɗinawa 32 Isra'ila ta kashe lokacin da suke kan layin karɓar kayan abinci a kusa da cibiiyoyi biyu ranar Asabar a Zirin Gaza, a cewar ma'aikatar lafiya da ke ƙarƙashin ikon Hamas.
Lamurran sun faru ne a Khan Younis da Rafah, inda aka jikkata wasu da dama a kusa da sansanonin da ƙungiyar GHF da Amurka ke goyon baya ke gudanarwa.
GHF ta ce babu abin da ya faru a wurin ko kuma kusa, amma kuma sojojin Isra'ila sun yi wasu ayyuka kafin a buɗe sansanonin.
Wani shaida ya faɗa wa kamfanin labarai na Reuters cewa wutar da sojojin Isra'ila suka buɗe ta yi kama da "yunƙurin kisa da gangan".
Kusan kullum sai an kashe Falasɗinawa a Gaza yayin da suke ƙoƙarin karɓar kayan tallafin abinci saboda yadda Isra'ilar ta hana shigar da komai da komai zirin, illa kayan da GHF ke rabawa.
.jpg)
No comments