Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Ɗaruruwan Falasɗinawa Na Fuskantar Barazanar Mutuwa Saboda Yunwa A Gaza - Likitoci

Likitoci a kudancin Gaza sun ce Falasɗinawa masu fama da yunwa da suke tururuwa zuwa cibiyoyin lafiya a yankin suna ƙaruwa. Daraktan asibiti...


Likitoci a kudancin Gaza sun ce Falasɗinawa masu fama da yunwa da suke tururuwa zuwa cibiyoyin lafiya a yankin suna ƙaruwa.

Daraktan asibitin Kuwaiti da ke Khan Younis ya ce marasa lafiya suna zuwa da alamun tsananin yunwa da rashin abinci mai gina jiki.

Sobaib Al-Hums ya yi gargaɗin cewa ɗaruruwan mutane suna fuskantar barazanar mutuwa saboda yunwar.

Cibiyar kare haƙƙin ɗan'adam ta Gaza ta ce ma'aikatan agaji tara ne Isra'ila ta kashe a lokacin da suke yunƙurin karɓar abinci mai gina jiki a kusa da Rafah a ranar Juma'a.

Abinci ƙadan ne kawai Isra'ila take bari yana shiga ziri Gaza - yawanci kuma ta Amurka kuma ake rabawa ƙarƙashin kulawar Isra'ila.

No comments