Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

An Yaba Wa Shugaba Tinubu Bisa Naɗa Muhammad Babangida A Matsayin Shugaban Bankin Noma Na Ƙasa

Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu yana ci gaba da samun yabo bisa sabbin naɗe-naɗen da ya yi, inda a ciki akwai amincewa da ya yi da naɗin Muh...


Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu yana ci gaba da samun yabo bisa sabbin naɗe-naɗen da ya yi, inda a ciki akwai amincewa da ya yi da naɗin Muhammad Babangida, ɗan tsohon Shugaban Mulkin Soja, Janar Ibrahim Badamasi Babangida, a matsayin Shugaban Hukumar Bankin Noma na Ƙasa (Bank of Agriculture), bayan sake fasalin bankin da aka yi.

A jiya Juma'a ne mai bai wa Shugaban Ƙasa shawara na musamman kan harkokin yaɗa labarai da dabarun sadarwa, Bayo Onanuga, ya fitar da wata sanarwa, inda ya bayyana cewa shugaban ya kuma amince da naɗin wasu shugabanni da daraktoci na hukumomin gwamnati guda bakwai.

Sauran waɗanda aka naɗa, kamar yadda ya ke ƙunshe cikin sanarwar, sun haɗa da:
    •    Lydia Kalat Musa (Daga Jihar Kaduna): Shugabar Hukumar Yankunan ’Yancin Kasuwanci na Man Fetur da Gas (Oil and Gas Free Zone Authority - OGFZA).
    •    Jamilu Wada Aliyu (Daga Jihar Kano): Shugaban Hukumar Nazarin Harshe da Ci gaban Ilimi (National Educational Research and Development Council - NERDC).
    •    Hon. Yahuza Ado Inuwa (Daga Jihar Kano): Shugaban Hukumar Tsarance da Daidaita Kayayyaki ta Ƙasa (Standard Organisation of Nigeria - SON).
    •    Sanusi Musa SAN (Daga Jihar Kano): Shugaban Cibiyar Zaman Lafiya da Warware Rikice-rikice (Institute of Peace and Conflict Resolution - IPCR).
    •    Prof. Al-Mustapha Alhaji Aliyu (Daga Jihar Sokoto): Darakta Janar na Hukumar Haɗin Gwiwar Fasaha a Afirka (Directorate of Technical Cooperation in Africa - DTCA).
    •    Sanusi Garba Rikiji (Daga Jihar Zamfara): Darakta Janar na Ofishin Najeriya kan Tattaunawar Kasuwanci (Nigerian Office for Trade Negotiations - NOTN).
    •    Mrs Tomi Somefun (Daga Jihar Oyo): Manajan Darakta na Hukumar Ci gaban Wutar Lantarki (National Hydro-Electric Power Areas Development Commission - HYPPADEC).
    •    Dr Abdulmumini Mohammed Aminu-Zaria (Daga Jihar Kaduna): Darakta Mai Gudanarwa na Hukumar Gudanar da Albarkatun Ruwa ta Ƙasa (Nigerian Integrated Water Resources Management Commission - NIWRMC).

Waɗannan naɗe-naɗe na nuna jajircewar Shugaba Tinubu na cike guraben shugabanci da mutane nagari domin tabbatar da ingantaccen aiki a hukumomin gwamnati.
 

No comments