Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Shugaba Tinubu Ya Bayyana Alhinin Rashe-rashen Da Aka Yi A Kano Da Mokwa

Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya bayyana alhini da jimami bisa mummunan hatsarin mota da ya rutsa da ‘yan wasan jihar Kano da ke kan hanya...


Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya bayyana alhini da jimami bisa mummunan hatsarin mota da ya rutsa da ‘yan wasan jihar Kano da ke kan hanyarsu ta dawowa daga Gasar Wasannin Kasa (National Sports Festival) da aka kammala a jihar Ogun.

A wata sanarwa daga Fadar Shugaban Ƙasa da mai ba da shawara kan harkokin labarai da dabarun sadarwa, Bayo Onanuga, ya fitar, shugaban ya ce wannan lamari babban rashi ne ga ƙasa baki ɗaya.

Shugaba Tinubu ya yi addu’ar Allah ya jikan wadanda suka rasu ya yi musu rahama, ya kuma bai wa iyalansu da al’ummar Kano hakuri da juriya bisa wannan babban rashi. Ya kuma bayyana cewa, hanya mafi dacewa da za a girmama waɗanda suka rasu ita ce a dauki matakan da za su rage aukuwar irin wannan hadurra a gaba.

Hakazalika, Shugaban Ƙasa ya nuna damuwa matuƙa kan ambaliya mai tsanani da ta afku a karamar hukumar Mokwa da ke Jihar Neja, wanda ya janyo mutuwar mutane da dama da kuma raba daruruwan iyalai da muhallansu.

“Ina miƙa ta’aziyya ta ga dukkan al’ummar Jihar Neja da iyalan waɗanda ambaliyar ta shafa. Wannan lokaci ne na jarrabawa, kuma muna tare da ku,” in ji Shugaba Tinubu

Bayan samun rahoton farko, Shugaban Ƙasa ya bayar da umarnin gaggawa na bude Cibiyar Amsar Gaggawa ta Ƙasa (National Emergency Response Centre), inda ya karɓi cikakken rahoto daga Hukumar kan girman ibtila’in da kuma bukatun gaggawa na jin ƙai da ake bukata.

A halin yanzu, an tura kayan agaji da ababen mafaka na wucin gadi ga mutanen da abin ya shafa, yayin da hukumomin tsaro suke aiki tukuru don ceto mutane da bada agajin gaggawa.

“Ina tabbatar wa da mutanen Mokwa cewa Gwamnatin Tarayya tana tare da ku, za mu ci gaba da aiki tare da Gwamnatin Jihar Neja don tabbatar da ceto cikin gaggawa da dawo da martabar rayuwar al’ummar yankin,” in ji Shugaban Tinubu

Ya kuma yi kira ga al’ummar Najeriya da su ci gaba da yi wa mutanen Mokwa addu’a a wannan lokaci mai tsanani.
 

No comments