Shugaban Kasuwar Sabuwar Panteka da ke garin Kaduna, Alhaji Aminu Abba Gwaska ya bayyana rashin gamsuwarsa dangane da yadda Wasu da ya kira ...
Shugaban Kasuwar Sabuwar Panteka da ke garin Kaduna, Alhaji Aminu Abba Gwaska ya bayyana rashin gamsuwarsa dangane da yadda Wasu da ya kira da gurɓatattun Alƙalan kotuna suke gudanar da harkokin shari'a a jihar Kaduna.
Alhaji Abba Aminu ya yi wannan zargi ne a wani taron manema labarai da ya ofishin sa da ke Kasuwar, inda ya yi zargin cin zarafinsa da wani Alƙali ya yi yayin da ya gurfana a gabansa domin kare kansa bisa wata shari'a da ta haɗo shi da wasu ɓata-garin matasa da ke gudanar da haramtacciyar sana'a a kasuwar ta sabuwar Panteka.
Alhaji Abba ya kuma yi zargi Alƙalin kotun da yin kama-karya da ƙarya da yi wa dokokin shari'a karen-tsaye.
A taron manema labaran da shugaban kasuwar sabuwar Panteka ya kira ya buƙaci gwamnatin jihar Kaduna a ƙarƙashin ma'aikatar Shari'a ta jihar da ta duba ayyukan wasu Alƙalan kotunan jihar a faɗin jihar.
Shugaban ya ce, '"Na kira wannan taron manema labarai ne domin na shaida wa Al'ummar jihar Kaduna yadda muke ƙoƙarin magance matsalar bata-gari a kasuwar sabuwar Panteka, wanda a irin matakin da muke ɗauka, inda muka dakatar da duk wasu yara masu gudanar da gurɓatacciyar sana'a a kasuwar.
"Kwanan baya lokacin tsohuwar Gwamnatin kasuwar, wani ɗan sanda mai suna ya kama wani ɓarawo wanda ya ce yana ba wasu 'yan panteka kaya, hakan ta sa muka bibiyi batun muka gano cewa yaran ɓarayi ne, kuma muka dakatar da su daga kasuwar domin hana aikata ɓarna.
"Amma daga baya sai aka samu wasu daga cikinsu suka ɗauki abin suka kai ƙara wata kotun Majistare suka Shigar da Shari'a da sunan shugaban kasuwar sabuwar Panteka da ɓata musu suna.
"lokacin da Alƙalin kotun ya kira ƙarar mu sai ya tambaye ni ga abin da da ake ƙara ta a kai, na ɓata wa wasu suna. Sai na ce ni ban ɓata wa wani suna ba, faɗin haka ke da wuya kawai sai ya ce a fitar da ni waje, ba tare da ya ba ni damar yin magana ba da kuma bincikar yadda ƙarar take ba.
"Sai ya yanke hukuncin a wuce da ni gidan Yari saboda na ɓata wa wasu suna. Shin abin tambaya a nan ta ina ne wanda ake ƙara ba za a ba shi damar kare kansa ba?
"Duk da cewa ni Basarake ne kuma Shugaban kasuwa, baya ga kuma kasancewata ni ɗan ƙasa ne, amma Alƙalin duk ya yi watsi da wannan, kawai ya zarta hukunci son ransa kawai."
Don haka a ƙarshe sai Shugaban Pantekar ya ce, "Muna kira ga Gwamna Uba Sani da ya dubi lamarin domin a tabbatar adalci akan batun. ''
Da wakilinmu ya tuntuɓi ma'aikatar ta jihar Kaduna, kuma sun tabbatar da cewa sun samu labarin ƙarar, amma za su yi dukkan mai yiwuwa domin yi wa kowanne ɓangare a adalci.
No comments