Daga Musa Muhammad Gwamnan Jihar Borno, Babagana Umara Zulum, ya yi alƙawarin ɗaukar nauyin karatun yaron da aka nuno a bidiyo ana cin zaraf...
Daga Musa Muhammad
Gwamnan Jihar Borno, Babagana Umara Zulum, ya yi alƙawarin ɗaukar nauyin karatun yaron da aka nuno a bidiyo ana cin zarafinsa, Bashir Gaji, tare da bayar da umurnin a gaggauta gurfanar da mutumin mai suna Bukar Modu don a hukunta shi.
Gwamna Zulum ya gana da ƙaramin yaron, Bashir Gaji, inda ya bayyana cewa gwamnati za ta samar wa mahaifiyar sa da gidan zama mai cikakken kayan more rayuwa, tare da tallafin karatu har zuwa matakin da ya ke buƙata.
Rahotanni sun nuna cewa an kama Bukar Modu ne a daren Asabar a Unguwar Umarari cikin Maiduguri, bisa umurnin Gwamna Zulum. Gwamnan ya bayar da wannan umurni ne ranar Lahadi yayin da ya gana da yaron, Bashir Gaji a fadar gwamnatin jihar.
Wannan bidiyon dai ya karaɗe kafafen sada zumunta, kuma ya tayar da ƙuraatuƙa, inda ya bayyana irin cin zarafin da yara ke fuskanta da kuma buƙatar ɗaukar mataki cikin gaggawa daga hukumomin tsaro da na shari'a.
A nasa ɓangaren, Gwamna Zulum ya jaddada cewa gwamnatinsa ba za ta lamunci duk wani nau’in cin zarafin yara ba, kuma ya buƙaci a tabbatar da cewa wanda ake zargi ya fuskanci hukuncin da ya dace da shi.
Gwamnan ya ce, “Wannan aika-aika ta ci karo da ɗabi’un mu, kuma cin amana ne ga nauyin da ke kan mu na kula da yara da ɗalibai. Ba za mu bar irin wannan cin zarafi ya ci gaba ba. Ina umartar hukumomi da su gaggauta ɗaukar mataki domin tabbatar da adalci. Yaran mu na da haƙƙin rayuwa cikin tsaro da samun tarbiyya.”
Haka kuma, Gwamna Zulum ya umarci Ma’aikatar Harkokin Mata da Ci gaban Jama’a da ta tsara shirye-shiryen wayar da kan al’umma, domin ilmantar da iyaye da malamai kan hanyoyin da suka dace na gyara tarbiyyar yara ba tare da cin zarafinsu ba.
Jaridar Matattarar Labarai ta gano cewa Iyalan yaron na zaune ne a sansanin 'yan gudun hijira da ke Monguno, bayan 'yan Boko Haram sun kashe mahaifinsa.
Ya zuwa haɗa rahoton nan dai, jama'a sai jinjina suka yi wa Gwamnan na jihar Borno bisa wannan mataki na gaggawa da ya ɗauka game da wannan zalunci, wanda aka ce zai iya zama darasi ga masu aikata irin wannan aiki.
No comments