Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Yadda 'Yan Bindiga Suka Sace Janar Na Soja A Katsina

Daga Musa Muhammad 'Yan ta'adda a Katsina sun sace Tsohon shugaban Hukumar 'yan yi wa ƙasa hidima NYSC, Birgediya Janar Maharazu...

Daga Musa Muhammad

'Yan ta'adda a Katsina sun sace Tsohon shugaban Hukumar 'yan yi wa ƙasa hidima NYSC, Birgediya Janar Maharazu Tsiga, tare da wasu da sama a garin na Tsiga. 

Jaridar Leadership ta ruwaito cewa da misalin ƙarfe 2:30 na dare ne 'yan bindigar suka shiga garin na Tsiga da ke Ƙaramar Hukumar Bakori ta jihar Katsina, suka wuce kai tsaye gidan Janar ɗin, inda suka yi awon gaba da shi, tare da wasu, sannan kuma suka rinƙa haɗawa da duk wanda suka ci karo da shi a hanyar su ta fita garin. 

Wata majiya ta bayyana cewa, ɓarayin sun shiga garin na Tsiga da yawan gaske, inda baya ga Tsohon Janar ɗin, 'yan ta'addan sun samu yin awon gaba da wasu manya a garin, tare da wasu da dama. 

Ya zuwa haɗa wannan rahoton dai ba a ji ɗuriyar su ba tukuna. 

No comments