Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Ministoci Za Su Fara Bayyana Wa Manema Labarai Irin Nasarorin Da Suka Samu

Ministocin gwamnatin Tinubu za su fara gabatar da ayyukan da suka yi ko suka sa a gaba a Tarukan Manema Labarai na Ministoci na shekarar 202...

Ministocin gwamnatin Tinubu za su fara gabatar da ayyukan da suka yi ko suka sa a gaba a Tarukan Manema Labarai na Ministoci na shekarar 2025 a ranar Juma’a, mai zuwa, 21 ga Fabrairu.

Ma'aikatar YaÉ—a da Wayar da Kai ce ta ba bayyana hakan, ta ce za a fara taron da Æ™arfe 11 na safe a Cibiyar Manema Labarai ta Ƙasa da ke Abuja.  

Ma'aikatar ta ce bisa umarnin Shugaba Bola Ahmed Tinubu, ministocin za su gabatar da rahoto kan nasarori, manufofi, da shirye-shiryen da suka aiwatar a ma’aikatun su.

 Ta Æ™ara da cewa wannan shiri yana nuna jajircewar gwamnati wajen tabbatar da gaskiya, riÆ™on amana, da hulÉ—a kai-tsaye da jama’a.

Za a fara jerin tarukan ne da gabatarwar Ministan Raya Kiwo, Mukhtar Maiha; da Ministan Cigaban Yankuna, Injiniya Abubakar Momoh.

Ma’aikatar ta gayyaci ‘yan jarida, masu ruwa da tsaki, da jama’a gaba É—aya don halartar wannan muhimmiyar tattaunawa da nufin bayyana wa jama'a irin cigaban da gwamnati ke samu.

 

No comments