Daga Hussaini Yero, Gusau Jam'iyyar Adawa ta APC a Jihar Zamfara na ƙalubalantar Rundunar 'Yan Sadan Jihar na nuna halin ko-in-kula...
Daga Hussaini Yero, Gusau
Jam'iyyar Adawa ta APC a Jihar Zamfara na ƙalubalantar Rundunar 'Yan Sadan Jihar na nuna halin ko-in-kula a duk lokacin da aka kai ma "Yan Jam'iyyar hari aka lalata kadarorin su da abubuwan hawansu a jihar.
Sakataren yaɗa labarai na Jam'iyyar APC na Jihar Zamfara Yusif Idris ne ya bayyana haka a takardar da ya sanya ma hannu ga manema labarai a Gusau.
A cewar sa, "Muna zargin "Yan Jam'iyyar PDP ne tare da 'Yan sakai, suka kai hari kan masu halartar bikin ƙaddamar da ayyukan Dan Majalisar wakilai mai wakiltar Maru/Bungudu a majalisar wakilai ta tarayya, Hon. Abdulmalik Zubairu Bungudu suka farfasa motocin su, kuma har zuwa yanzu babu wani matakin kamo waɗanda suka yi wannan ta'addanci daga Rundunar 'Yan Sadan wannan kuma ba shi ba ne karo farko da aka mana ba.
"‘Yan ta’addan sun fito fili a dabaru sun tsaya kan titin Gusau/Bungudu domin kai harin wanda ya kai ga lalata motoci da dama tare da raunata wadanda ke cikin motar saboda kawai ‘yan Jamiyyar APC ne.
"Don haka jam’iyyar APC reshen jihar Zamfara tana Allah wadai da wannan harin, tare da roƙon ‘yan sanda da sauran jami’an tsaro da su gaggauta ɗaukar mataki ta hanyar damƙe waɗanda suka aikata wannan aika-aika tare da gurfanar da su gaban ƙuliya ga abin da suka aikata, ko kuma daga yanzu za a tilasta mana mu kare kanmu daga duk wani ko ƙungiyar da ta kai kaima hari.
"Akan haka muke kira ga mambobinmu da su yi haƙuri domin jam’iyya za ta tabbatar da yin adalci ga duk waɗanda aka kai wa hari da waɗanda suka jikkata ko aka lalata musu dukiyoyi."

No comments