Daga Ibrahim Muhammad, Kano Gwamnan jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya sanar da rasuwar shugaban hukumar kula da tsaftar muhalli ta jih...
Daga Ibrahim Muhammad, Kano
Gwamnan jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya sanar da rasuwar shugaban hukumar kula da tsaftar muhalli ta jihar (REMASAB), Alhaji Ahmadu Haruna Zago.
Hakan na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa ya fitar a safiyar ranar Alhamis.
Marigayi Zago wanda aka fi sani da Ɗan Zago ya rasu ne a safiyar ranar Alhamis yana da shekaru 74 a duniya bayan ya sha fama da jinya a asibitin koyarwa na Aminu Kano.
A cewar Sunusi Bature Dawakin Tofa, marigayi Ɗan Zago ya rasu ya bar mata huɗu, ‘ya’ya 37, da jikoki da dama.
Majiyar ‘yan uwan mamacin ta tabbatar da cewa a yau ne da misalin ƙarfe 1:00 na rana aka yi Sallar jana’izarsa (Salatul Janaza) a fadar Sarkin Kano, inda ‘yan uwa da jami’an gwamnati da abokan arziki da sauran ‘yan uwa da abokan arzikin marigayin ɗan siyasar suka hallara don yin bankwana.
Gwamna Yusuf ya nuna matuƙar alhininsa kan wannan rashi, inda ya bayyana Alhaji Zago a matsayin ma’aikaci mai ƙwazo, pwararre mai dabarun siyasa, kuma hamshaƙin ɗan kasuwa wanda ya taka muhimmiyar rawa wajen tsara yanayin siyasar Kano cikin shekaru 50 da suka gabata.
Ya kuma miƙa ta’aziyyarsa ga iyalan mamacin da kuma al’ummar Kano, yana mai addu’ar Allah ya jikansa da rahama.
Alhaji Ahmadu Haruna Zago wani ɗan siyasa ne na musamman mai dimbin goyon bayan talakawa wanda ya yi ayyuka da dama ciki har da shugaban jam'iyyar ANPP ta jiha.
Ya kuma kasance mai baiwa tsohon gwamnan jihar Kano shawara kan harkokin siyasa, mataimaki na musamman ga tsohon kakakin majalisar wakilai, kuma mamba a kamfanoni masu zaman kansu da dama a ciki da wajen jihar Kano.

No comments