Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

EFCC Ta Bayyana Wuraren Da Za Ta Yi Gwanjon Motoci 850 Da Ta Ƙwace

Daga Musa Muhammad  Hukumar yi wa tattalin arziki zagon ƙasa ta EFCC ta bayyana cewa ta kammala duk shirye-shiryen da suka wajaba don gwanjo...

Daga Musa Muhammad 

Hukumar yi wa tattalin arziki zagon ƙasa ta EFCC ta bayyana cewa ta kammala duk shirye-shiryen da suka wajaba don gwanjon wasu motoci guda 850, waɗanda ta ce ta ƙwato daga hannun waɗanda aka kama da laifin babakere da dukiyar jama'a 

Hukumar ta ce gwanjon motocin zai gudana ne a wuraren da suka haɗa da Kano, Abuja da Fatakwal, kuma ma'aikatan Hukumar, tare da waɗansu ƙwararru a harkar gwanjo da aka zaɓo ne za su gudanar da aikin. 

Hukumar ta kuma bayyana cewa waɗannan motoci da za a yi gwanjon su, sun haɗa da motoci na alfarma manya-manya, matsaikata da kuma irin su Toyota Camry. Ta ce ta ƙwato su ne a wajen gudanar ayyukanta daban-daban, da suka haɗa da almundahanar kuɗaɗe, cin hanci da rashawa, da kuma masu zamba ta hanyar yanar gizo (cybercrime).

Ta ce za ta gudanar da gwanjon waɗannan motoci ne kamar yadda yake ƙunshe a kundin dokar da ta kafata, ta ' EFCC (Establishment) Act, 2004, Public Procurement Act, 2007 and the Proceeds of Crime (Recovery & Management) Act, 2022.

Cikin wata sanarwa da Hukumar ta fitar, ta bayyana cewa, “Hukumar @officialEFCC, ta hanyar wasu ƙwararru a harkar gwanjon kayayyaki, za ta gudanar da wani gwanjon motoci ta hanyar yanar gizo (e-Auction), waɗanda masu su suka bar wa gwamnati, kamar yadda dokar da ta kafa mu ta tanada."

 

No comments