Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

WATSA NAIRORI A BIKI: EFCC Ta Gayyaci Ango da Uwar Amarya

Daga Musa Muhammad Hukuma yaƙi da yi wa tattalin arzikin ƙasar nan zagon ƙasa ta EFCC ta yi ƙarin haske game da Bidiyon da ke yawo a Soshial...

Daga Musa Muhammad

Hukuma yaƙi da yi wa tattalin arzikin ƙasar nan zagon ƙasa ta EFCC ta yi ƙarin haske game da Bidiyon da ke yawo a Soshial Mediya, inda aka nuna ana watsi da Nairori a wani bikin aure da aka yi a Birnin Kano a ranar Juma'a 24 ga watan da ya gabata na Oktoba. 

Cikin wata sanarwar da mai magana da yawun Hukumar, Dele Oyewale ya sanya wa hannu, ya ce Hukumar ta ce, a wannan Bidiyon da ke yawo an nuna cewa abin ya faru ne a bikin 'yar Tsohon Gwamnan jihar Gombe, Sanata Ɗanjuma Goje, wato Fauziya Danjuma Goje. 

EFCC ta ce, bayan da ta ga wannan hoto sai ta shiga bincike, inda daga bisani ta gano cewa abin ya faru ne a bikin auren Amina Babagana Zannan a wannan rana, amma ba wai a bikin 'yar Sanata Ɗanjuma Goje ba.  

Amina Zanna 'yar wata hamshaƙiyar 'yar kasuwa ce mai sana'ar sayar da gwala-gwalai a Abuja, Kano da kuma Dubai, wato Hajara Seidu Haruna (da ake wa laƙabi da Hafsat Gold Nigeria), ita ce kuma shugabar kamfanin 'Hafsat Jewellery Enterprise'.

Hajiya Hafsat Haruna ta amince cewa a bikin ɗiyar ta ne aka yi wa Naira wannan cin mutuncin, amma ta ce Angon ɗiyar tata, Ibrahim Mohammad mutumin ƙasar Nijar ne, kuma duk waɗanda suka yi liƙi da Nairori da Daloli a bikin, 'yan uwansa ne daga can Nijar. 

Hukumar ta EFCC ta ce yanzu dai ta gayyaci wannan Ango ya kai kansa babban ofishinta da ke Abuja, tare da duk wanda ya san ya watsa waɗannan kuɗaɗe a bikin nasa da Zannah. 

A ƙarshe Hukumar ta nuna godiyarta ga duk waɗanda suka nuna damuwarsu game da wannan cin mutunci da aka yi wa Naira. Ta ce, tana nan wajen ganin ta ladabtar da duk wanda ke keta alfarmar Naira, mutum ko shi waye.

 

No comments