Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Gwamna Abba Kabir Mai Biyayya Ne Ga Tsarin Tafiyar Kwankwasiyya -Muhammad Jamu

Daga Ibrahim Muhammad, Kano An bayyana  Gwamnan jihar Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf da cewa a tsaye yake da ƙafarsa a cikin biyayya ga tsarin...

Daga Ibrahim Muhammad, Kano

An bayyana  Gwamnan jihar Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf da cewa a tsaye yake da ƙafarsa a cikin biyayya ga tsarin tafiyar Kwankwasiyya.

Mai bai wa Gwamnan jihar Kano shawara na musamman akan harkokin cikin gida da  ƙasashen waje da hulɗa da jama'a, Hon. Muhamnad Jamu Yusuf ya bayyana ne ya bayyana hakan a wata zantawa da wakilin mu a Kano. 

Inda ya ce, a cikin jihar Kano gaba ɗaya, daga shi Muhammad Jamo sai Injiniya Abba Kabir Yusuf suke da kamanni iri ɗaya a harka ta siyasa ta gidan jagora Injiniya Rabiu Musa Kwankwaso.

Ya  ce, domin sai da abokan siyasar jagoransu Kwankwaso da yawa suka rabu da shi a lokacin da ya tsayar da Gwamna Abba Kabir Yusuf  ya zama ɗan takarar Gwamna, suke ganin cewa kamar an ɗauko shi a matsayin yaro da bai wuce  maitaimakawa na musamman ba, wanda bai isa komai ba, suna ganin su ne suka fi dacewa da iyawa.

Ya ƙara da cewa, sai suke ganin an ɗauki wani mutum ƙasa da su wanda bai kai su ba, an tsayar da shi takarar Gwamna, saboda haka suka rabu da tafiyar siyasar Kwankwaso. 

Jamu ya ci gaba da cewa bayan wannan, sai shi   a lokacin da suke jam'iyyar PDP, Kwankwaso ya tsayar da shi a matakin shugaban jam'iyyar PDP na shiyyar Arewa maso Yamma, a wancan lokacin abokan tafiyarsa da yawa sai da suka yi fushi saboda suna ganin shi yaro ne da bai kai ko'ina ba, saboda haka me ya sa za a ɗauko shi a tsayar da shi kan wannan, suka rabu da Kwankwaso.

Saboda haka sai Hon.Muhamnad Jamu Yusuf  ya ce sun san irin jajircewa da Kwankwaso ya yi akan su shi da Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf. Saboda haka ba za su taɓa yi wa Kwankwaso butulci ba, da yardar Allah domin, masoyin su ne su ma masoyansa ne.

Don haka Muhammad Jamu Yusuf ya Jaddada cewa duk wani da yake ganin zai iya yin wani abu domin raba tafiyar Injiniya Rabiu Musa Kwankwaso da Abba Kabir Yusuf da masoyansa, ba zai yi nasara ba, suna fata a ƙarƙashin tafiyar Kwankwasiyya Injiniya Abba Kabir Yusuf  zai shekara 8 a Gwamnan Jihar Kano da yardar Allah. 

 

No comments