Daga Ibrahim Muhammad, Kano An yi kira ga al'ummar jijar Kano da ma ķasar nan baki ďaya su yi karatun ta-natsu su sake jaraba jam'iy...
Daga Ibrahim Muhammad, Kano
An yi kira ga al'ummar jijar Kano da ma ķasar nan baki ďaya su yi karatun ta-natsu su sake jaraba jam'iyyar PDP domin ota ce kaďai za ta dawo musu da walwala da sauķin rayuwa, su ďauke su daga inda APC ta ajiye su, ta mayar da su tashar da suka bar su cikin walwala da sauķin rayuwa.
Sabon Mataimakin shugaban jam,iyyar PDP na shiyyar Kano ta tsakiya, Alhaji Kabiru Bello Ďandago ne ya yi wannan kiran a wata tattaunawa da ya yi da wakilin ku, inda ya ce ko a wani taro na masu ruwa da tsaki na jam'iyyar ya ce a shekara ta 2015 sai da suka gargaďi jama'a da cewa kar a kori jam'iyyar PDP daga kan mulki, domin sun san abin da ta tsara, amma mutanen Nijeriya suka ķeķasa ķasa suka ķi, saboda yaudarar da aka yi musu.
Ya ce, yanzu kowa ya duba aljihunsa da tukunyar sa, mace ta gaya wa mijinta irin ķunci na halin rayuwa na zamantakewa da suke gani tun daga 2015 da jam'iyyar PDP ta bar Gwamnati zuwa yanzu.
Ya ķara da cewa a lokacin mulkin Gwamnatin PDP ana sayar da buhun Shinkafa N8,000, amma yanzu fa? Kwanon shinkafa ya gagari talakawa.
Alhaji Kabiru Bello Ďandago ya ce a matsayin sa na matsimakin shugaban jam'iyyar PDP a shiyyar Kano ta Tsakiya ya ce yadda aka gudanar da zaɓe aka gama lafiya babbar nasara a gare su a jam'iyyar.
Don haka ya ja hankalin 'yan jam'iyyar PDP su sani jam'iyyar ta su ba ta shugabanni ba ce kadai, ta duk 'ya'yan jam’iyyar ne, da sauran duk wanda ya amince da ita, hatta mai zae in ya yarda da ita shi ma ya zama mai ruwa da tsaki a cikinta.
Alhaji Kabiru Bello ya ce zai gabatar da ayyukan da za su zama na samun c igaba ga jam'iyyar a jihar Kano. Zaben fitar da shugabannin jam'iyyar da aka gudanar ya yi wa wasu dadi wasu kuma akasin haka ,amma su a matsayin su na sabbin shugabanni aikinsu na farko shi ne su yi rarrashi da bayar da hakuri da saka ci gaban jam'iyyar a gaba.

No comments