Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Ofishin Uwargidan Gwamnan Zamfara Da Hukukar Agile Za Su Bunƙasa Ilimin 'Ya'ya Mata A Jihar

  Daga Hussaini Yero, Gusau Ofishin Uwargidan Gwamnan Zamfara, Hajiya Huriyya Dauda Lawal, tare da haɗin gwiwa da Hukumar AGILE sun ɓullo da...

 

Daga Hussaini Yero, Gusau

Ofishin Uwargidan Gwamnan Zamfara, Hajiya Huriyya Dauda Lawal, tare da haɗin gwiwa da Hukumar AGILE sun ɓullo da wani shiri na musamman na bunƙasa Ilimin 'ya'ya Mata a faɗin jihar don ceto rayuwar su daga halin da suke cikin na rashin zuwa makaranta.

A jawabin ta, Matar Gwamnan jihar Zamfara ta bayyana  cewa a cikin wannan watan ne Majalisar Ɗinkin Duniya ta ayyana ranar 11 ga Oktoba a matsayin ranar yara mata ta duniya don amincinsu da 'yancin 'ya'ya mata da magance ƙalubalen zuwan su makaranta.

Hajiya Huriyya ta ce, "Gwamnatinmu ta sanya ilimi a kan gaba a cikin ƙudurorin ta  guda shida, tare da mai da hankali sosai wajen ganin an bai wa ‘ya’ya mata ilimi mai inganci a matsayin hanyar da za ta kai ga samun haske a gobe.

"Mun yi imanin cewa idan 'yan matanmu za su yi nasara a duniyar yau, dole ne su sami  ingantaccen ilimi, musamman a fannoni kamar Kimiyya, Fasaha, Injiniya, da Lissafi wanda ke cikin shirin (STEM).

"Kuma wannan shirin wani yunƙuri ne na haɗin gwiwa tsakanin ofishina da (AGILE), Shiri ne da  Taimakon Bankin Duniya da Ma'aikatar Ilimi ta Tarayya.

"Maƙasudin wannan shirin shi ne don inganta ilimin sakandare da samar da ɗakin gwaje-gwaje a Makarantun Sakandare na ’yan mata da kayan aikin gwaje-gwaje na zamani a matsayin wani ɓangare na ƙoƙarinmu na haɓaka karatun tsarin STEM.

 "A ƙarshe ina jaddada aniyar gwamnatin mai girma Gwamna Dauda Lawal na tallafa wa shirin ilimantar wa ‘yan mata na (AGILE) da kuma ƙudinlrin sa na bunƙasa ilimin ‘ya’ya mata da ƙarfafa musu gwiwa, tare za mu ci gaba da ƙarfafa waɗannan tsare-tsare tare da tabbatar da cewa kowace yarinya a jiharmu ta sami damar yin karatu da kammala shi.

No comments