Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Ƙungiyar Shugabannin Jam'iyyun Siyasar Arewa Ta Jinjina Wa Hon. Liman

  Ƙungiyar Shugabannin Jam'iyyun Siyasa ta Arewa ta yaba wa Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Kaduna, kuma Shugaban ƙungiyar majalisun Dok...

 

Ƙungiyar Shugabannin Jam'iyyun Siyasa ta Arewa ta yaba wa Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Kaduna, kuma Shugaban ƙungiyar majalisun Dokokin jihohin Arewa, Hon. Yusuf Dahiru Liman a kan nasarar da ya samu a majalisar.

Ƙungiyar na miƙa godiya da jinjina ga Shugaban Majalisar Dokokin Jihar Kaduna ne bisa jajircewarsa da jagorancin da ya nuna wajen zartar da wasu muhimman ƙudirori guda huɗu a baya-bayan nan.

Babban Sakataren ƙungiyar, Mikailu Abubakar a cikin wata sanarwar da ya fitar, ya bayyana hakan ne ga manema labarai a Kaduna, ya ce a rana mai cike da tarihi, Majalisar Dokokin Jihar Kaduna ta nuna ƙwarewa da jajircewa wajen ci gaban jihar ta hanyar zartar da ƙudirori kamar haka:

1. Hukumar Kula da Hanyoyi ta Kaduna (KADRA). 

2. Hukumar Kula da hanyoyin Karkara ta Kaduna (KADRARA). 

3. Hukumar Kula da Kuɗaɗen Hanya ta Kaduna (KADSRFAB).

4. Hukumar Tattara Kuɗaɗen Hanya ta Kaduna (KADSRF). 

Mallam Abubakar ya ce, "waɗannan ayyuka na majalisar na nuna irin namijin ƙoƙarin da shugabannin mu ke yi wajen ba da fifiko wajen samar da ababen more rayuwa da inganta hanyoyin sufuri a Jihar Kaduna.

"Ƙaddamar da waɗannan kuɗaɗen na nuna wani muhimmin mataki na haɓaka tattalin arziƙi da tabbatar da jin daɗin ’yan jihar."

Ƙungiyar ta kuma yaba da haɗin kai da masu ruwa da tsaki suka nuna a wannan gagarumin abin a-yaba, ta ce, "Irin wannan shugabanci zai zaburar da sauran yankuna wajen yin koyi da shi.

"Muna miƙa godiya ta musamman ga Shugaban Majalisar Dokokin Jihar Kaduna, Hon. Yusuf Dahiru Liman, da ɗaukacin 'yan majalisar dokokin jihar bisa jajircewar da suke yi na ci gaba da bunƙasar jihar Kaduna da ma yankin Arewa gaba ɗaya."

No comments