Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

'Yan Bindiga Na Kashe Waɗanda Suka Kama A Abuja Don An Yi Jinkirin Biyan Kuɗin Fansa

Masu garkuwa da mutane, waɗanda suka sace mutum 10 a rukunin gidajen Sagwari da ke garin Dutse na yankin Abuja, sun sake kashe mutum buyi da...

Masu garkuwa da mutane, waɗanda suka sace mutum 10 a rukunin gidajen Sagwari da ke garin Dutse na yankin Abuja, sun sake kashe mutum buyi daga cikin waɗanda ke hanun su, don yin gargaɗi ga 'yan uwan waɗanda ke hannun su kawo kuɗin fansa. 

Bayan wannan ɗanyen hukunci, 'yan bindigar sun kuma ƙara kuɗin fansa a kan kowanne daga ciki, inda suka ce yanzu sai an biya Naira Miliyan 100 ga kowane mutum ɗaya, maimakon Naira Miliyan 60 da suka sanya tun da fari. Yanzu suna neman Naira Miliyan 700 ke nan. 

Mazauna wannan rukunin gidaje, sun bayyana cewa 'yan bindigar sun kashe mutanen ne saboda kawai an samu jinkiri wajen biyan kuɗin fansar. 

Rahotannin da suka fito, suna nuni d cewa wata yarinya 'yar kimanin shekara 13, wacce ke makarantar sakandare, mai su a Folorunsho Ariyo na cikin waɗanda aka kashe. 

In dai ba a manta ba, a 'yan kwanakin nan ne 'yan bindigar suka shiga wasu ƙauyuka da ke yankin Bwari na Abuja, inda suka tafi da wasu yan shida 'yqn gida ɗaya, har suka kashe ɗaya daga cikin su, wacce aka bayar da sunan ta da Nabeeha Al-Kadriyar, wanda sun yi haka ne don su tilasta wa iyalan su biya kuɗin da suka ƙayyade na fansa.

No comments