Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Zaɓe A Jihohin Kogi, Imo Da Bayelsa: Shugaban 'Yan Sanda Ya Aika Da Mataimakan Sa Uku, Za A Taƙaita Zirga-zirga

  Sufeto Janar na 'yan sandan Nijeriya, Kayode Egbetokun ya aika da manyan mataimakan sa guda uku, waɗanda za su sanya ido don ganin an ...

 

Sufeto Janar na 'yan sandan Nijeriya, Kayode Egbetokun ya aika da manyan mataimakan sa guda uku, waɗanda za su sanya ido don ganin an gudanar da zaɓe cikin kwanciyar hankali a zaɓen Gwamna na ranar Asabar mai zuwa a jihohin Kogi, Imo da Bayelsa, ya kuma bayar da umurnin a taƙaita zirga-zirga a lokutan zaɓen.

Manyan mataimakan masu muƙamin DIG da za su gudanar da wannan aiki, sun haɗa da DIG Habu Sani wanda zai kula da jihar Kogi, sai Sokari-Pedro zai kula da Bayelsa, sannan Frank Mba a Imo.

Sufeton 'yan sandan ya ba su umurnin cewa su ne za su jagoranci sauran manyan jami'an da ke yankin, masu muƙaman AIG da kuma Kwamishinnoin 'yan sandan.

Kakakin rundunar 'yan sandan na ƙasa, ACP Olumuyiwa Adejobi ne bayyana haka cikin wata sanarwa, inda ya ƙara da cewa Sufeton ya kuma amince da bayar da wasu motoci guda 220 don sauƙaƙa zirga-zirga ga jami'an a waɗannan jihohi.

Haka kuma akwai jirage masu saukar unguwa guda biyar da za a yi aiki da su, akwai kuma wasu jiragen ruwa guda 15 don aiki a yankunan da ke da ruwa.

Kakakin 'yan sandan ya bayyana cewa babbar manufar su ta aiki, ita ce samar wa da al’umma yanayi mai kyau da za su sami damar gudanar ayyukan su na 'yan ƙasa cikin kwanciyar hankali, ba tare da wata ƙuntatawa ba.

Daga nan sai ya bayyana cewa sun samar da wasu lambobi na waya, waɗanda za a iya kira a duk lokacin da aka ga wani abu da zai iya tayar da hankalin jama'a.

Waɗannan lambobi su ne, Jihar Imo– 08034773600 or 08113659301. Jihar Kogi – 07038329084. Jihar Bayelsa – 07034578208 09167322691

No comments