Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Cikakken Jawabin Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinub A Taron Kasa Na Jam'iyyar APC

Jam'iyyar APC ta gudanar da babban taronta na ƙasa jiya a Abuja inda ta zaɓi sabbin shugabannin jam'iyyar, ga cikakken jawabin shuga...


Jam'iyyar APC ta gudanar da babban taronta na ƙasa jiya a Abuja inda ta zaɓi sabbin shugabannin jam'iyyar, ga cikakken jawabin shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu a wajen taron, kamar yadda Dokin Ƙarfe TV ta ruwaito:

"A yau, ina tsaye a gabanku zuciyata cike da godiya, alfahari, da fata. Godiya ga Allah Maɗaukaki saboda ni’imarsa ga ƙasarmu da jam’iyyarmu. Alfahari da abin da muka gina tun 2013, da kuma fatan makoma mai kyau duk da ƙalubalen da muke fuskanta.

Wannan taron na APC karo na huɗu ba kawai taro ba ne; wani muhimmin babi ne a tarihin dimokaraɗiyya da jam’iyyarmu. Taron yana ba mu dama mu ƙarfafa haɗin-kai, sake tabbatar da muradinmu, da sake rungumar ƙa’idojin da suka haɗa mu tun farko.

Taken Taro: “Haɗin Kai A Cikin Ci Gaba: Ƙarfafa Ajandar Sabunta Fata.” Wannan taken na tuna mana cewa babu ci gaba ba tare da haɗin-kai ba.

Shekaru goma sha uku da suka wuce, mun yi jarumta wajen haɗa kanmu don ceto ƙasa daga matsalolin tattalin arziƙi na lokacin.

Mun yi imani cewa ƙasar na iya zama mafi girma idan dimokaraɗiyya ta yi aiki ga kowa, shugabanci ya dogara ne akan hangen nesa, ladabi, adalci, da ci gaba.

Mun tuna da shugabannin da suka kafa jam’iyyar, matasa, mata, da sauran membobi waɗanda suka yi ƙoƙari wajen gina wannan dandali.

Mun yi jimamin rasuwar shugaba Muhammadu Buhari da sauran shugabanni da suka riga mu, muna roƙon Allah ya jikansu.

Babban ƙarfimmu bai taɓa zama a girmanmu ba, sai dai haɗin-kai. Jam’iyyun siyasa ba sa faɗuwa ne kawai ta sakamakon zaɓe; sau da yawa suna faɗuwa idan son kai ya rinjayi ra’ayi ko muradi ya maye gurbin ladabi. Wannan taro na nuna cewa APC tana da ƙarfi, haɗin kai, da nufin ci gaba.

Jam’iyyar ba kawai don samun nasarar ƴan siyasa ba ce; an kafa ta ne don sauya ƙasa, tabbatar da cewa gwamnati na aiki, tsaro ya tabbata, talauci ya ragu, kuma kowa zai iya rayuwa da daraja da fata.

Mun yi imani da adalci da gasa mai inganci; jam’iyya mai adalci na buƙatar hamayya mai inganci wadda za ta iya tambaya da taimaka wa wajen inganta manufofi. Duk da haka, wasu ƙungiyoyin hamayya suna tsangwamar Dokar Zaɓe ta 2026, abin da ba shi da amfani ga jama’a.

Tun da aka sake zabarmu a 2023, mun himmatu wajen aiwatar da Ajandar Sabunta Fata. Mun fuskanci ƙalubale masu wuya, amma mun samu nasarori a fannin: hanyoyi, tashoshin jiragen ruwa da filayen jiragen sama, manufofin haraji da kuɗaɗen shiga, da tsaro. Haka kuma, an samu bunƙasar kasuwanci, raguwar hauhawar farashi, da karuwar amincewar masu zuba jari.

Duk da haka, har yanzu akwai matsaloli kamar: wutar lantarki da tsohon tsarin watsa wutar, wanda za a magance ta hanyar kafa kamfanin wuta na Grid Asset Management Company wanda zai ƙara megawat 1,600 a sabon layi.

Matasa su ne fata da makomar ƙasa. Dole ne jam’iyya ta ba su damar shiga fagen yanke shawara, ba kawai matsayin kayan ado ba. Mata kuma su kasance cikin shugabanci da tsara manufofi. Jam’iyya mai ƙarfafa mata za ta fi ƙarfi.

Kammalawa:

Ina kira ga duk masu zaɓe da shugabanni su yi aiki da gaskiya, haɗin-kai, da sadaukarwa. Duk wanda aka zaɓa ya yi jagoranci da ƙarfin zuciya, gaskiya, da hangen nesa. Ci gaban APC da dimokaraɗiyyar Najeriya sun dogara da wannan jagoranci.

Allah ya albarkaci jam’iyya mu,
Allah ya albarkaci Ƙasar Tarayyar Najeriya.

Nagode". In ji shugaban ƙasa Bola Tinubu.

Shugaba Tinubu kuma gode wa kwamitin shirya taron, ƙarƙashin jagorancin Aminu Bello Masari, da Sanata Anyim Pius Anyim, GCON, bisa ƙoƙari da nagartarsu wajen tsara taron.

Sannan ya yaba wa gwamnonin da suka taka rawa wajen shirya taron, musamman: Gwamna Abdulrahman Abdulrazaq (Kwara), Mataimaki na II, Gwamna Mai Mala Buni (Yobe), Sakataren Taro, Gwamna Hope Uzodimma (Imo), Ma’aji.

Ya kuma yaba wa Gwamna Dapo Abiodun, shugaban Kwamitin Shirya Wurin Taro, bisa jajirce wa da gudunmawarsa wajen shigar da taron cikin tsari da kammalawa.

Haka kuma, ya jaddada godiyarsa ga duk sauran Gwamnoni da Ministoci kan haɗin-kai da ƙoƙarinsu wanda ya tabbatar da nasarar taron.
 

No comments