Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Ƙungiyar Tarayyar Afirka Ta Gargaɗi Amurka Kan Tsoma Baki Cikin Lamurran Nijeriya

Ƙungiyar Tarayyar Afirka (AU) ta bayyana goyon bayanta ga cikakken ikon Nijeriya kan harkokin ta na cikin gida tare da tabbatar da ’yancin a...


Ƙungiyar Tarayyar Afirka (AU) ta bayyana goyon bayanta ga cikakken ikon Nijeriya kan harkokin ta na cikin gida tare da tabbatar da ’yancin addini da bin doka da oda a ƙasar, inda ta gargaɗi Amurka da ta tsame bakin ta.

A wata sanarwa da Hukumar Tarayyar Afirka (AUC) ta fitar, ta jaddada cewa tana da cikakken kishin kiyaye dokokin da ke cikin kundin kafa ƙungiyar, musamman kan batun ikon ƙasa, rashin katsalandan, da ’yancin addini.

Hukumar ta ce ta damu da wasu kalamai daga gwamnatin Amurka da ke zargin gwamnatin Nijeriya da hannu wajen kashe mabiya addinin Kirista a ƙasar, da kuma barazanar kai farmakin soja kan ƙasar.

A cewar sanarwar, Nijeriya na daga cikin mambobin AU masu muhimmanci waɗanda ke taka rawar gani wajen tabbatar da zaman lafiya, yaƙi da ta’addanci, da haɗin kai a Nahiyar.

“AU tana mutunta cikakken ikon Nijeriya wajen tafiyar da lamurran tsaron ta, tsaron ƙasa, da ’yancin addini bisa tsarin kundin mulki da ƙa’idojin ƙasa da ƙasa,” in ji sanarwar.

Hukumar ta ce ta amince da matsayar da gwamnatin Nijeriya ta sha nanatawa cewa kundin tsarin mulkin ƙasar yana baiwa kowane dan kasa ’yancin yin addinin da yake so, kuma gwamnati ba ta amince da wani nau’in wariya ko zaluncin addini ba.

Ta kuma jaddada cewa matsalolin tsaro da Nijeriya ke fuskanta na da sarkakiya, suna shafar mabiya addinai daban-daban, ciki har da matsalar ta’addanci, satar mutane, rikicin kabilanci da rikicin makiyaya da manoma.

Hukumar ta yi kira da a kara hadin kai tsakanin ƙasashen yankin da abokan hulɗa na ƙasa da ƙasa domin taimaka wa Nijeriya da sauran kasashen Afirka wajen ƙarfafa matakan tsaro, kare rayuka, da gurfanar da masu aikata laifuka.

“Ya zama wajibi a guji amfani da addini a matsayin makami na siyasa ko bayanin da zai iya haifar da rikici,” in ji AUC.

Hukumar ta kuma bukaci kasashen waje, musamman Amurka, da su ci gaba da tattaunawa da Najeriya ta hanyar diflomasiyya, musayar bayanan tsaro, da taimakon ci gaban ƙwarewa maimakon barazanar kai farmaki, wanda ka iya barazana ga zaman lafiyar nahiyar.

A ƙarshe, Hukumar Tarayyar Afirka ta tabbatar da aniyarta ta ci gaba da tallafawa kasashen mambobinta wajen tabbatar da zaman lafiya, kare hakkin dan Adam, da cigaban tattalin arziki, tare da mutunta ikon kowace kasa da ka’idar rashin tsoma baki.

 

No comments