Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Ma’aikatar Yaɗa Labarai Da Haɗin Gwiwar Hukumar Ƙididdiga Na Jihar Kaduna Sun Ƙulla Yarjejeniya

Ma’aikatar yaɗa labarai ta Jihar Kaduna ta ƙulla wata yarjejeniyar haɗin gwiwa da Hukumar Ƙididdiga ta Jiha (BoS) domin shirya horo na musam...


Ma’aikatar yaɗa labarai ta Jihar Kaduna ta ƙulla wata yarjejeniyar haɗin gwiwa da Hukumar Ƙididdiga ta Jiha (BoS) domin shirya horo na musamman ga ’yan jarida akan yadda za su rinƙa bayar da rahotanni da bayanan ƙididdiga.

Manufar wannan shirin, shi ne cike gibi tsakanin bayanan gwamnati masu rikitarwa da fahimtar jama’a, domin inganta gaskiya, ɗaukar nauyi da kuma ƙarfafa hulɗa tsakanin al'umma da harkokin mulki.

An ƙaddamar da wannan haɗin gwiwar ne a ranar Talata lokacin da Babban Jami’in Hukumar Ƙididdiga ta Jiha, Dakta Bukar Baba Alhaji, ya kai ziyarar ban-girma ga Kwamishinan yaɗa labarai  Malam Ahmed Maiyaki, a offishin sa.

Dakta Bukar ya bayyana wannan haɗin gwiwar a matsayin abu mai muhimmanci wanda ya zo a kan gaba wajen ƙarfafa wayar da kan jama’a game da rawar da sahihan bayanai suke takawa wajen tsara ci gaba da samar da manufofi masu tushe, da ɗorewar ci gaban ƙasa.

Dakta Bukar, ya jaddada muhimmancin haɗin gwiwa da kafafen yaɗa labarai wajen isar da bayanan Hukumar ga al’umma.

A cikin jawabin sa, Kwamishinan yaɗa labarai Malam Ahmed Maiyaki, ya yaba da wannan shiri tare da tabbatar da cikakken goyon bayan Ma’aikata rsa ga manufofin Hukumar.

Ya ce samar da sahihan bayanai da kafa gwamnati mai adalci, wacce da dogara da adalci, yana daga cikin manufofi da ƙudirorin gwamnatin jihar Kaduna wanda hakan zai taimaka wajen kawo ci gaba ga al’umma baki ɗaya.
 

No comments