Gwamnatin Jihar Kaduna ta bayyana sabon salo na samar da zaman lafiya ta hanyar bai wa tsofaffin ‘yan bindiga damar samun ilimi, kula da laf...
Gwamnatin Jihar Kaduna ta bayyana sabon salo na samar da zaman lafiya ta hanyar bai wa tsofaffin ‘yan bindiga damar samun ilimi, kula da lafiya da kuma hanyoyin dogaro da kai, maimakon amfani da ƙarfin soja.
Kwamishinan Yaɗa Labarai na jihar, Malam Ahmad Maiyaki, ne ya bayyana hakan yayin taron kwana ɗaya kan aikin jaridar zaman lafiya, wanda Ƙungiyar ’Yan Jarida ta NUJ ta shirya tare da haɗin gwiwar Global Peace Foundation Nigeria da ma’aikatar yaɗa labarai ta jihar Kaduna.
Ya ce, wannan sabon tsari da ake kira “Kaduna Peace Model” ya mai da hankali ne kan tattaunawa da fahimtar juna, ba tare da amfani da ƙarfi ko biyan kuɗin fansa ba. A cewar sa, manufar ita ce dawo da martabar ɗan adam, gina amincewa da fahimtar juna tsakanin al’umma domin kawo ƙarshen laifuka.
Maiyaki ya ce, “Ba za ka iya haɗa bom da zaman lafiya ba; dole ne ka gina shi da amincewa.”
Ya ƙara da cewa, sauyin ya fara ne lokacin da shugabannin ‘yan bindiga suka roƙi gwamnati ta sake buɗe kasuwanni, makarantu da cibiyoyin lafiya da aka rufe saboda matsalar tsaro. Gwamnatin ta amince, saboda waɗannan abubuwa buƙatu ne na yau da kullum, ba biyan kuɗin fansa ba.
Ya bayyana cewa tsakanin shekarar 2015 zuwa 2023, an samu fiye da 1,160 hare-hare a Kaduna wanda ya yi sanadin mutuwar mutum 4,876, da dubban da aka sace ko suka rasa muhallansu. A shekarar 2021 kaɗai, an kashe mutane 1,192 tare da sace 3,348, abin da ya sa aka rufe makarantu 142 da cibiyoyin lafiya 192.
Kwamishinan ya ce duk da cewa a baya ƙasashen waje sun kira Kaduna “red zone”, yanzu gwamnati na gina sabuwar amincewa ta hanyar hanyar zaman lafiya ba ta soja ba, tare da haɗin gwiwar Ofishin Mai Ba Shugaban Ƙasa Shawara kan Tsaro (ONSA).
A cewarsa, ta hanyar wannan haɗin gwiwa, mutane sama da 500 da aka sace sun kubuta cikin aminci ba tare da an biya kuɗin fansa ko amfani da ƙarfin soja ba.
Maiyaki ya ƙara da cewa, “Yanzu muna ganin amincewa inda tsoro ya mamaye, da haɗin kai inda gaba take.”
Jihar Kaduna na daga cikin wuraren da matsalar ‘yan bindiga ta fi ta’azzara a Nijeriya. Kwanan nan, ‘yan ta’adda sun kashe ’yan sanda biyu a ofishin rundunar ‘yan sanda na garin Zonkwa, hedikwatar ƙaramar hukumar Zangon Kataf a Kudancin Kaduna.
.jpg)
No comments