A wani muhimmin matakin ci gaba, Kamfanin Ƙera Buhunan Siminti da sauran buhuna da ledodji na rukunin Ɗangote ‘Dangote Packaging Limited’ (D...
A wani muhimmin matakin ci gaba, Kamfanin Ƙera Buhunan Siminti da sauran buhuna da ledodji na rukunin Ɗangote ‘Dangote Packaging Limited’ (DPL) ya ƙaddamar da wasu na’urori na zamani domin bunƙasa fasaharsa.
Aikin kamfanin shi ne ƙera buhunan siminti da sukari, ledojin taliya da dai sauran su.
A wajen ƙaddamar da sabuwar fasahar ne a ranar Laraba, Manajan Darakta kuma Babban Jami’in Gudanarwa na DPL, Sai Prakash ya bayyana muhimman abubuwan da sabbin injinan ke da su tare da bayyana su a matsayin sabuwar fasahar zamani.
Ya ƙara da cewa, samar da waɗannan injuna babbar nasara ce kuma za ta taimaka wajen inganta sana’o’i da kuma inganta buhunan da ake ƙerawa daga Kamfanin Obajana.
Hakazalika, Manajan Daraktan Rukunin Kamfanin Simintin Dangote, Arvind Pathak, wanda ya halarci bikin ya yaba da sabon aikin.
Ya yi ishara da cewa, an samu gagarumin sauyi a tsawon shekarun da aka fara samar da buhunan siminti, kuma ya yi imanin cewa sabbin fasahohin za su cike gibin da aka gano wajen samar da buhuna masu inganci.
Shi ma da yake nasa jawabin, babban jami’in kamfanin Simintin Dangote, Sunil Mahajan, da Daraktan ayyuka na Siminti Ɗangote, Anandam Duraisamy, waɗanda suma suka halarci bikin sun yi na’am da hakan tare da bayyana fatan za a samu ci gaba a cikin kwanaki masu zuwa ta fuskar samar da ingantaccen buhunhunan siminti kuma cikin adadi mai yawa.
A nasa bangaren, Daraktan Kamfanin Simintin Dangote na Obajana, Engr Azad Nawabuddin ya yi fatan cewa waɗannan sabbin injinan za su inganta ayyukan DPL da DCP sosai, ya kuma ƙara jaddada goyon bayan DCP Obajana ga ayyukan DPL ta kowace hanya.
A jawabinsa na maraba tun da farko, Babban Manaja na Dangote Packaging Limited da ke Obajana, Peter Dickson, ya ce: “A yau, mun tsaya domin shaida sabuwar fasahar zamani, inda muke sa ran za mu kai wani matsayi mai girma tare da taimakon wannan fasaha ta zamani.”
Dickson ya ce, na'urorin na da saurin gaske, inda suka yi daidai da zamanin da muke ciki.
No comments