Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

RUSAU A KADUNA: Ina Da Cikakkun Takardun Mallaka, Amma Aka Rushe Mani Gida - Injiniya Gilima

Duk da halin da ake ciki na ƙuncin rayuwa, sai ga shi a ranar Lahadin da ta gabata Hukumar Raya Birane ta jihar Kaduna (KASUPDA), ta rusa gi...


Duk da halin da ake ciki na ƙuncin rayuwa, sai ga shi a ranar Lahadin da ta gabata Hukumar Raya Birane ta jihar Kaduna (KASUPDA), ta rusa gidan wani Injinyan gine-gine, wanda kuma ya ce ya mallaki wurin fiye da shekaru 20.

Wannan gida da ke lamba 11, Titin Yahaya Imam da ke Malali a Kaduna, mallakin Injiniya Yahaya Gilima ne, wanda ya ce ya mallake shi da cikakkun takardu tun a shekarar 2002, inda aka fara aikin ginawa nan take, sannan aka kammala a shekarar 2003.

Sai dai kuma a ranar Juma’ar da ta gabata, kwatsam sai suka wayi gari an liƙa masu wata sanarwa a jikin bangon gidan, inda ake neman da su kwashe duka kaya gidan cikin sa’o’i 48 ko kuma a rushe tare da su.

A wani taron manema labarai da ya gabatar a harabar gidan a Kaduna, Injiniya Gilima ya bayyana mamaki da takaicinsa kan lamarin, inda ya ce an kawo masa sanarwar ne a ranar Juma'a, ranar da ba a zuwa aiki a jihar Kaduna, wanda hakan ya sa ya kasa bayar da amsa nan take.

“Ina jiran ranar Litinin ne ta yi in gabatar da ƙorafina ga sanarwar da KASUPDA ta liƙa a jikin gida, amma sai suka zo da misalin ƙarfe 11 na dare tare da jami'an tsaro a cikin shirin yaƙi, suka kore mu daga gidan, suka fara rusawa” inji shi.

Lamarin dai ya jawo cece-kuce da tofin Allah ya tsine a jihar, inda da dama ke kallon hakan a matsayin take ’yancin Injiniya Gilima a matsayinsa na ɗan Nijeriya na mallakar fili ko gida ba tare da tsangwama ko tsoratarwa ba. An nuna damuwa game da ayyukan gwamnati da 'yancin 'yan ƙasa.

Injiya Gilima ya ci gaba da bayyana cewa, shi dai abin da ya sani shi ne sun kwashe kimanin shekaru tara suna shari'a da wani mutum wanda ya taɓa aiko masa cewa wai filin sa ne, wanda kuma yanzu haka maganar tana kotu.

"Saboda haka ni na yi mamakin ganin yadda gwamnatin ta ɗauki wannan mataki alhali maganar na gaban ƙuliya.

"Hukumar KASUBDA sun taɓa kawo mana takardar cewa mu kawo takardun shaidar mallakar wannan, na tattara takardun na je na same su, na ce masu ma maganar tana kotu. 

Wannan ne ya sa muka yi mamakin yadda gwamnatin ta tsallake kotu ta ɗauki wannan mataki. 

"Amma duk da za mu ci gaba da bin hanyoyin shari'a kamar yadda doka ta tana domin ƙwato mana 'yanci. Domin mu ma 'yan ƙasa ne kamar sauran jama'a," inji Injiniya Gilima.

A nata ɓangaren, Hukumar KASUBDA ta bayyana cewa akwai mai wannan wuri, wanda kuma tun a shekarun baya ya kawo masu shaidunsa a rubuce, sun nemi Injiniya Gilima ya zo a tattauna don a samu matsaya, amma ya yi biris.

No comments