Daga Ibrahim Muhammad, Kano Shugaban rukunin kamfanonin Ɗangote, Alhaji Aliko Ɗangote, ya nuna damuwarsa game da kuɗin ruwa na kusan kashi 3...
Daga Ibrahim Muhammad, Kano
Shugaban rukunin kamfanonin Ɗangote, Alhaji Aliko Ɗangote, ya nuna damuwarsa game da kuɗin ruwa na kusan kashi 30 cikin 100 da babban bankin Nijeriya ya ƙara ga masana'antu, yana mai kira ga gwamnati da ta tallafa wajen haɓaka kamfanoni.
Ya bayyana hakan ne a taron ƙungiyar masu masana'antu na ƙasa da aka yi a Abuja, inda ya yi gargaɗin cewa, “Babu wanda zai iya samar da ayyukan yi da kuɗin ruwa na kashi 30 babu wani ci gaba da za a samu.
Daga nan Attajirin ya jaddada buƙatar samar da kuɗaɗe da kuma Samar da kariya ga masana’antun cikin gida su ƙara haɓaka domin rage dogaro da shigo da kaya, wanda hakan yana ƙara haifar da fatara da rashin ayyuka.
Alhaji Aliko Ɗangote ya jaddada muhimmancin tallafa wa masana’antu na gida don yaƙar rashin tsaro da samar da wadatar arziki.

No comments