Daga Hussaini Yero, Funtua Uwargidan Shugaban Ƙasa, Sanata Oluremi Tinuba a makon nan ta raba wa mata ɗalibai 'yan Sakandare su dubu ɗa...
Uwargidan Shugaban Ƙasa, Sanata Oluremi Tinuba a makon nan ta raba wa mata ɗalibai 'yan Sakandare su dubu ɗaya tallafin Audugar Tsaftace Jiki, wanda za su yi amfani da ita har na tsawon shekara guda domin tsaface jiki a lokacin da suke al'ada.
Uwargidan gwamnan Zamfara Hajiya Huriyya Dauda Lawal ce ta wakilce ta a lokacin ƙaddamar da rabon, wanda ya gudana a makarantar GGDSS da ke Tudun Wada Gusau.
A jwabin ta, Sanata Oluremi Tinuba ta bayyana cewa, "A yau mun haɗu ne domin ƙaddamar da shirin Renewed Hope Initiative mai take “Flow with Confidence”, wani muhimmin shiri da aka ƙirƙira domin tallafa wa ‘yan mata, musamman ɗalibai, ta hanyar koya musu tsaftace jinin al’ada, kare mutuncin su da kuma ƙarfafa musu gwiwa.
"Wannan shiri yana daga cikin muhimman manufofin da ke ƙarƙashin shirin Renewed Hope Agenda na mai girma shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu.
"Shirin “Flow with Confidence” an riga an ƙaddamar da shi a wasu jahohin ƙasar nan, yau kuma jihar Zamfara ce ke ƙaddamar nata shirin. Wannan na nuna cewa gwamnatin tarayya tana son ganin kowace yarinya a kowane yanki ta samu damar kula da tsafta da mutuncin ta ba tare da wata tangarɗa ba.
"A yau muna cikin wani zamani da bai kamata wata yarinya ta daina zuwa makaranta ba, saboda ba ta da kuɗin sayen kayan tsaftar jinin al’ada ba. Abin takaici ne cewa har yanzu akwai ‘yan mata da dama, musamman a ƙauyukka, da ke fuskantar matsaloli lokacin al’ada, wasu ma sukan daina zuwa makaranta gaba ɗaya saboda wannan dalili. Wannan lamari ya zama dole mu kawo ƙarshen sa, kuma wannan shiri ne da aka samar da shi domin magance irin wannan matsala.
"A ƙarƙashin wannan shiri, za a rarraba kayan tsaftar jinin al’ada ga ‘yan mata dubu ɗari ukku da saba'in (370,000) a faɗin ƙasar nan. Kowace jaha da Babban Birnin Tarayya za su samu kunshi dubu goma (10,000) na kayan tsafta. Wannan taimako ne musamman ga ‘yan mata na ƙauyukka da ba su da ƙarfin saye.
"A yau, a nan jahar Zamfara, zan miƙa kunshi dubu goma (10,000) na kayan tsafta domin rabawa ‘yan mata 10,000, kowacce yarinya za ta sami abin amfani da zai isheta har shekara guda.
"Mun zaɓi kayan tsaftar da ake jefarwa bayan amfani (disposable pads) saboda tsaftar su, sauƙin amfani, da kuma kariya ga lafiyar macce.
"A shirin mu na Renewed Hope Initiative (RHI), muna da yaƙinin cewa ba za a taɓa barin yarinya ta zubar da iliminta da mutuncinta ba. nasarar wannan shiri tana hannun mu gaba ɗaya, kuma muna kira ga shugabannin ƙananan hukumomi da su ɗauki nauyin tabbatar da cewa kayan sun isa ga ‘yan mata na ƙauyukka kai tsaye, ba tare da an sayar da su ba.
"A Renewed Hope Initiative, an kashe naira biliyan 2 da miliyan ɗari biyu da ashirin wajen sayen waɗannan kayan daga kamfanin cikin gida mai suna Uniglory Nigeria Limited da ke Ikorodu, Legas.
"Wannan yana nuna yadda gwamnati ke ƙarfafa masana’antun cikin gida da kuma kula da buƙatun ‘yan ƙasa. Saboda haka ina kira ga hukumomi, kamfanoni, da ‘yan Nijeriya masu kishin ƙasa da su shiga cikin wannan shiri domin taimakawa ‘yan mata masu buƙata.
Ina kuma roƙon sarakunan gargajiya, malamai, da shugabannin al’umma da su ba da goyon baya ga wannan shiri, su sa ido wajen rabon kayan, su kuma tabbatar da cewa ‘yan matan mu suna amfani da su yadda ya kamata. Hakan zai taimaka wajen ganin sun girma cikin tsafta, ilimi, da kima.
Ga ku ‘yan matan mu da za ku amfana da wannan taimako, wannan kyauta ce ta musamman a gare ku. kada ku sayar da kayan, ku ci gaba da zuwa makaranta, ku dage da karatu, ku taimaki juna. Ku yi amfani da wannan dama domin cika burinku, domin ku ne matan gobe ta Nijeriya.
A ƙarshe, Sanata Oluremi tayi kira ga kowa da kowa da mu ɗauki alhakin kare mutunci, lafiya, da makomar ‘yan mata a ƙasarmu. Mu tabbatar kowace yarinya tana da damar rayuwa cikin kwanciyar hankali, samun ilimi da ci gaba.

No comments