Gwamnatin Jihar Zamfara ta kammala shirye-shiryen bikin auren gata ga sama da marayu 200 a jihar. Sakataren Hukumar Zakkah da Tallafi ta jih...
Gwamnatin Jihar Zamfara ta kammala shirye-shiryen bikin auren gata ga sama da marayu 200 a jihar.
Sakataren Hukumar Zakkah da Tallafi ta jihar, Malam Habibu Balarabe, ne ya bayyana hakan ga manema labarai a Gusau.
Ya ce, za a gudanar da bikin a ranar Litinin, 23 ga Nuwamba, 2025, a harabar hukumar.
Balarabe ya ce, an kammala tantance duk waɗanda za su amfana da shirin ɗaurin auren, kuma an zaɓe su bisa cancanta.
Baya ga bikin auren, hukumar za ta bai wa mata 200 da ke sana'o'in hannu tallafin kuɗi domin ƙarfafa rayuwarsu da kasuwancinsu.
Ya ƙara da cewa, mata 100 sun kammala horo na makonni uku a fannin kiwon kaji, kuma za a ba su kayan fara sana'a domin su fara aiki.
Hakanan, hukumar ta shirya biyan bashin wasu mutane da ke gaban kotunan shari’a da cibiyoyin gyaran hali a faɗin jihar.
Sakataren ya kuma bayyana cewa wasu marayu sun samu horo kan ilimin kwamfuta, kuma za a ba su kayan aiki lokacin bikin.
Shirye-shiryen auren gatan ba sabon abu ba ne a Arewacin Nijeriya, domin a ‘yan shekarun baya gwamnatoci da shugabanni sun riƙa amfani da wannan hanya wajen tallafa wa marasa galihu.

No comments