Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

2027: Ba Mu Da Hujjar Da Ba Za Mu Zabi Gwamna Uba Sani Da Shugaba Tinubu Ba — Ramalan Yero

Tsohon gwamnan jihar Kaduna Dakta Mukhtar Ramalan Yero, ya bayyana cewa al’ummar jihar Kaduna basu da wata hujja ko dalilin da zai sa su yi ...


Tsohon gwamnan jihar Kaduna Dakta Mukhtar Ramalan Yero, ya bayyana cewa al’ummar jihar Kaduna basu da wata hujja ko dalilin da zai sa su yi watsi da Gwamna Uba Sani ko Shugaba Bola Ahmed Tinubu a zabukan da ke tafe.

Dakta Ramalan Yero , ya bayyana haka ne a jawabin da ya gabatar yayin kaddamar shugabannin ƙungiyar ‘Uba Sani Alheri Ne‘ na jihar Kaduna ƙarƙashin jagorancin Dakta Bashir Idris  Lifidan Jama’a Wanda ya gudana a ɗakin taro na gidan Arewa.

Dallatun Zazzau, ya ce shugabancin Uba Sani da na Tinubu ya nuna kwararan hujjoji na jajircewa wajen inganta rayuwar al’umma, samar da tsaro da kuma aiwatar da manufofi masu amfani ga kasa da jihoha.

Ya bayyana cewa a jihar Kaduna, gwamnan Uba Sani ya nuna kwarewa wajen tafiyar da harkokin gwamnati cikin natsuwa, sauƙaƙe rayuwa ga talakawa, da kuma rungumar tsarin mulki mai mutunta ‘yancin jama’a. Ya kara da cewa sauye-sauyen da ake gani a fannoni kamar kiwon lafiya, ilimi, tsaro da harkokin noman  sun sa jama’a da dama suka fara ganin sauyi a zahiri a wurare daban-daban a fadin jihar.

Game da gwamnatin tarayya kuwa, tsohon gwamnan ya ce Shugaba Tinubu ya fara aiwatar da nauyukan gyare-gyare masu tsauri, wadanda za su bukaci hakuri da fahimtar jama’a, tare da tabbatar da cewa tsarin tattalin arziki da manufofin kasa suna samun karbuwa a duniya.

Ya ce, “A matsayinmu na shugabanni, ba mu da wata dalili da zai sa mu ce ba za mu zabi Tinubu ko Uba Sani ba. Ayyukan da suke aiwatarwa da hangen nesan da suke dashi suna da muhimmanci ga cigaban al’umma.”

Tsohon gwamnan ya kuma bukaci ‘yan siyasa da su kauce wa yada maganganu marasa tushe, su mayar da hankali kan gaskiya da neman mafita ga matsalolin jama’a.

Hakazalika, ya bayyana goyon bayan sa da irin matakin da kungiyar da dauka fara tallata manufofin gwamnatin Uba Sani Da Bola Tinubu ga lungu da sako na jihar Kaduna baki daya.
 

No comments